Yadda wasu yara suka kashe mahaifyarsu a lokacin da suke fada da juna

Yadda wasu yara suka kashe mahaifyarsu a lokacin da suke fada da juna

Idan ajali ya yi kira, ko ba ciwo sai an je, kamar yadda yan Hausa suke fada, a nan ma wata mata mai suna Ngodoo ce ta gamu da ajalinta bayan ta yanke jiki ta fadi a lokacin da take tsaka da raba fada tsakanin yaranta biyu.

Daily Trust ta ruwaito wannan lamari mai ban ta’ajibi ya faru ne a gidanta dake kan titin sabon kasuwan zamani a cikin garin Makurdi, babban birnin jahar Benuwe a ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kaduna ta yi nadin sabon shugaba a hukumar jin dadin alhazai

Rahotanni sun bayyana cewa matar, wanda ta kammala shirin fara karatun digiri na uku a jami’ar noma ta gwamnatin tarayya dake Makurdi ta rasu ne a daidai lokacin da danta dan shekara 28 yayi kokarin daba ma kanwarsa wuka.

Haka zalika rahotannin sun bayyana cewa dan matar mai suna Dominic ya yi kaurin suna a unguwarsu a matsayin mai yawan neman fada, kuma dan daba, wanda hakan ya dade yana ci ma babarsa tuwo a kwarya.

Da majiyarmu ta tuntubi rundunar Yansandan jahar Benuwe domin samun karin bayani game da bahallatsar, sai mai magana da yawunta, DSP Catherine Anene ta bayyana cewa tuni sun kama yaron, kuma sun fara bincikensa.

A wani labarin kuma, akalla mutane uku ne suka mutu a sakamakon wata rikita rikita da ta kunno kai a kan wata kujerar sarauta a cikin karamar hukumar Ankpa ta jahar Kogi,.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu gidajen sarauta guda biyu ne suke jayayya a kan wannan kujerar sarauta wanda aka dade ana zaban wanda zai hauta a tsakaninsu, toh amma a wannan karo lamarin ya ta’azzara, har ta kai ga zubar da jini da asarar dukiya.

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne a daren Laraba, 29 ga watan Janairu a kan wannan kujerar sarauta ta ‘Onu Akwu’, sai dai ba daga ranar aka fara jayayyar ba, sun dade kowa na ikirarin lokacinsa ne ya fitar da sarki, wanda har ta kai su ga kotu.

“Muna cikin barci sai muka ji hayaniya daga yankin gabashin garinmu, a lokacin da na fito sai na tarar wasu gidaje suna ci da wuta.” Kamar yadda wani mazaunin garin, kuma ganau ba jiyau bay a bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel