Wata sabuwar cuta ta kama mutane 4 a Benuwe, ta kashesu har lahira
A yayin da ake fama da bullar cutar zazzabin Lassa a Najeriya, wata sabuwar annoba ta bayyana a jahar Benuwe, yankin Arewa maso tsakiyan Najeriya, kuma har ta halaka akalla mutane hudu.
Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wannan cuta ta bulla ne a kauyen Oye-Obi dake cikin karamar hukumar Obi ta jahar Benuwe, kamar yadda shugaban kungiyar matasan kabilar Igede, Andyson Iji Egbodo ya bayyana.
KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Rundunar Sojan sama ta tura wani sabon jirgi yaki zuwa Maiduguri
Andyson ya bayyana haka ne a daren Laraba a madadin sauran jama’an kauyen, inda yace a yanzu haka akwai mutanen kauyen 15 da suka kamu da wannan cuta kuma an kwantar dasu a asibiti bayan nuna alamomin wannan cuta.
“Cutar ta kashe mutane 4 zuwa yanzu a cikin makonni biyu, mamatan sun hada da Happiness Ogbu, Onah Ogbedu, Andy Edu da Wisdom Agwo, kafin mutuwarsu dukkaninsu sun yi fama da ciwon kai, zafin cikin jiki, zawo, amai, ciwon ciki, kasalan jiki da kuma kumburin ciki.” Inji shi.
Da wannan ne Andyson ya yi kira ga gwamnatin jahar Benuwe da sauran hukumomin kiwon lafiya dasu kai musu dauki tun kafin cutar ta cigaba da wanzuwa, kuma har ta janyo karin mace macen mutane.
Wani babban jami’I a ma’aikatar kiwon lafiyan jahar, Dakta Sam Ngishe ya tabbatar da bullar cutar, kuma ya tabbatar da mutuwar mutane 4 da suka kamu da cutar, sai dai yace tuni sun tura jami’an bada agajin gaggawa zuwa kauyen, kuma saun dauke mutane uku da suka kamu da cutar zuwa Makurdi domin bincikensu.
Dakta Sam idan ba an kammala gudanar da bincike ba, ba zai iya tabbatar da ko wani irin ciwo bane wannan, musamman saboda wasu yan garin sun ce kamar an sanya guba a ruwan garin ne, yayin da wasu ke cewa zazzabi ne mai zafi.
A wani labarin kuma, likitoci bakwai da ma’aikatan jinya biyar ne suke karkashin kulawa bayan an kebancesu a cibiyar kiwon lafiya na gwamnatin tarayya dake garin Yola, babban birnin jahar Adamawa, sakamakon sun yi mu’amala da mutanen dake dauke da cutar zazzabin Lassa.
Wata mata mai dauke da juna biyu ne take dauke da cutar, sai dai bata samu nasarar haihuwa ba, inda ta yi barin cikinta, jami’an kiwon lafiya sun kamu da cutar ne a lokacin da suka kwantar da ita a sashin haihuwa, inda suka cire mahaifarta.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng