Rikicin Tiv da Jukun: An rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin Benuwe da Taraba
Manyan kusoshin gwamnatin jihar Benuwe da na jihar Taraba sun rattaba hannu a kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya a jihar Nasarawa.
An rattaba hannu a kan yarjejeniyar ne domin kawo karshen yawan samun barkewar rikici a tsakanin kabilun Tivi da Jukun.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da aka aikawa manema labarai ranar Laraba.
Takardar na dauke da sa hannun Injiniya Haruna Manu, mataimakin gwamnan jihar Taraba da Injiniya Benson Anounu, mataimakin gwamnan jihar Benuwe.
Sun rattaba hannu a kan takardar ne a gaban Dakta Emmanuel Akabe, mataimakin gwamnan jihar Nasarawa.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ne ya bude taron saka hannu a takardar yarjejeniyar a gaban masu ruwa da tsaki daga jihohin Benuwe da Taraba.
A cikin takardar sanarwar, an bayyana cewa, "an kulla yarjejeniyar ne domin tabbatar da samun tsagaitawar hare-hare a tsakanin kabilun domin samun zaman lafiya a tsakaninsu.
"Gwamnonin jihohin biyu za su yi aiki tare da ma su rike da sarautun gargajiya domin wayar da kan jama'a a kan bukatar samun zaman lafiya da zai bawa mazauna sansanin 'yan gudun hijira (IDPs) damar dawowa gidajensu.
DUBA WANNAN: FG ta janye shirin bayar da tallafin N20,000 a jihohi hudu
"Za a yi amfani da kafafen sadarwa wajen isar da sakon bukatar zaman lafiya ga jama'a domin tabbatar da dawowar mazauna sansanin gudun hijira gidajensu."
Ragowar sauran sharudan da ke cikin yarjejeniyar sun hada da tabbatar da mayar da 'yan Taraba mazauna IDP gidajensu domin su noma gonakinsu a lokacin damuna.
A cikin takardar, an shawarci gwamnatocin Benuwe da Taraba a kan bukatar su hada kai wajen yakar ta'addanci da 'yan ta'adda a jihohinsu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng