Shekaru 2 da Hukuncin Kotun Koli, Gwamnoni na Zuba Kudin Kananan Hukumomi a Aljihun Jiha
- Kusan shekara biyu bayan hukuncin Kotun Koli, har yanzu jihohi da dama na ci gaba da sarrafa kudin kananan hukumomi ta asusun hadin gwiwa
- Rahotanni sun nuna an ware wa kananan hukumomi Naira tiriliyan 10.48 tsakanin Yulin 2024 zuwa Yunin 2026, wanda kuma kudin bai shiga hannunsu ba
- NULGE ta i kuka da cewa har ce har yanzu gwamnatin tarayya ba ta fara tura kudin da ake raba wa wa daga FAAC kai tsaye zuwa asusun kananan hukumomi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja – Kusan shekara biyu bayan Kotun Koli ta umarci gwamnatin tarayya ta rika tura kudin rabon FAAC kai tsaye zuwa asusun kananan hukumomi 774 na Najeriya.
Amma wani bincike ya nuna har yanzu ba a aiwatar da hukuncin yadda ya kamata ba a yawancin jihohin kasar wanda ke da nasaba da yadda wasu gwamnoni suka ki tsarin.

Source: Facebook
Binciken jaridar Punch ya nuna cewa an ware wa kananan hukumomi jimillar Naira tiriliyan 10.479 tsakanin Yulin 2024 zuwa Yunin 2026.
Ana cece-kuce kan kudin kananan hukumomi
Duk da wannan karin kudi, har yanzu ana ta cece-kuce kan ko ana tura su kai tsaye zuwa asusun kananan hukumomi kamar yadda Kotun Koli ta umarta a hukuncinta na ranar 11 ga Yulin 2024.
Kotun ta haramta wa gwamnatocin jihohi rike ko kashe kudin da aka ware wa kananan hukumomi, tare da bayyana cewa nada kwamitocin rikon kwarya maimakon zababbun shugabanni ya sabawa kundin tsarin mulki.
Sai dai binciken ya nuna cewa jihohi da dama na ci gaba da amfani da Asusun Hadin Gwiwar Jiha da Kananan Hukumomi, lamarin da ke nuna cewa har yanzu kananan hukumomi ba su samu cikakken ikon tafiyar da kudinsu ba.
A cikin watanni 12 na farko bayan hukuncin, an ware wa kananan hukumomi Naira tiriliyan 4.496. Wannan ya karu zuwa Naira tiriliyan 5.984 a shekara ta biyu, karin kusan Naira tiriliyan 1.488, wato karin 33.1%.

Kara karanta wannan
PFIPC: Shugaban hukumar bogi ya soki binciken ICPC, ya aika sako ga Shugaba Tinubu
NULGE ta koka kan kudin kananan hukumomi
Kungiyar Ma'aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa (NULGE) ta ce har yanzu gwamnatin tarayya ba ta fara aiwatar da umarnin Kotun Koli ba.
Shugaban NULGE na kasa, Aliyu Kankara, ya ce duk da rubuce-rubucen da kungiyar ta aikawa gwamnati, har yanzu ana ci gaba da tura kudin kananan hukumomi ta hannun jihohi.

Source: Twitter
Ya ce ba za a iya cewa an samu cikakken 'yancin cin gashin kan kananan hukumomi ba har sai an fara tura kudin kai tsaye zuwa asusunsu.
Binciken ya nuna cewa a jihohin Kaduna, Kano, Benue, Plateau da Sokoto, har yanzu gwamnatocin jihohi ne ke kula da rabon kudin kananan hukumomi.
Tinubu ya fusata kan batun kananan hukumomi
A baya, kun samu labarin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nunawa gwamnoni cewa ba da wasa yake ba kan 'yancin kananan hukumomi ba, musamman wajen tabbatar da yancinsu.
Shugaba Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin su aiwatar da hukuncin Kotun Koli wanda ya umarci a sakarwa kananan hukumomi mara wajen barinsu su sarrafa kudinsu kai tsaye ba tare da sa baki ba.
Shugaban kasar ya fito kai tsaye ya gayawa gwamnonin matakin da zai dauka idan har ba su aiwatar da hakan ba musamman bayan ganin cewa dokar kasa ta bayar da umarnin a bar masu kudinsu.
Asali: Legit.ng
