Yanzu Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da zaben gwamna Ortom

Yanzu Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da zaben gwamna Ortom

- Kotun koli ta tabbatar da zaben gwamna Samuel Ortom na jihar Benue

- Babbar kotun ta kuma yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar, Emmanuel Jime ya daukaka kan nasarar gwamna Ortom

- Jime dai na kalubalantar zaben gwamna Ortom ne a matsayin gwamnan Benue a zaben watan Maris, 2019

Kotun koli a yau Talata, 21 ga watan Janairu ta tabbatar da zaben gwamna Samuel Ortom na jihar Benue.

Babbar kotun, da take zartar da hukunci ta hannun kwamitinta na alkalai bakwai karkashin jagorancin Justis Olabode Rhodes-Vivour, ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar, Emmanuel Jime ya daukaka kan nasarar gwamna Ortom na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Justis Sylvester Ngwuta wanda ya karanto hukuncin, ya ce kwamitin bai ga dalilin rashin amincewa da hukuncin kotunan zabe da na daukaka kara da suka dawo da Ortom a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris, 2019 ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tabbatar da Salih-Farah a matsayin Shugaban NITT

A wani labari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa alkalai masu shari'a sun tabbatar da Simon Bako Lalong matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Plateau.

Kotun ta raba gardamar ne bayan watanni goma da hukumar gudanar da zabe INEC ta alantashi matsayin zakaran zaben 9 ga Maris, 2020.

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta Jeremiah Useni, sun shigar da kara kotu ne domin kalubalantar nasarar APC a zaben.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel