Iran Ta Fusata da Amurka da Kai Wasu Hare Hare Kusa da Asibiti a Kasar Musulunci

Iran Ta Fusata da Amurka da Kai Wasu Hare Hare Kusa da Asibiti a Kasar Musulunci

  • Hare-haren da Amurka ta kai yankin wani asibitin da ake kula da masu fama da cutar daji ya fusata gwamnatin kasar Iran
  • Rahoto ya nuna cewa marasa lafiya 211 sun bar asibitin masu cutar daji cikin gaggawa bayan harin na kasar Amurka
  • Iran ta bayyana harin a matsayin "ta'asa" da ta haddasa firgici ga marasa lafiya, duk da babu rahoton mutuwar kowa zuwa yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Fiye da marasa lafiya 200 ne aka kwashe daga Asibitin Kwararru na Baghaei da ke kudancin Iran bayan hare-haren da Amurka ta kai a yankin.

Daraktan asibitin, Reza Bazar, ya ce hare-haren da aka kai birnin Ahvaz sun sa asibitin wanda ke dauke da masu fama da cutar daji fiye da 200, ya daina aiki.

Kasar Iran.
Hayaki na tashi bayan waus hare-haren da Amurka ta kai birnin Tehran a watan Maris, 2026 Hoto: Atta Kenare
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta wallafa rahoton cewa ba a samu rahoton mutuwar kowa ba sakamakon harin, amma an kwace duka marasa lafiya daga aibitin.

Kara karanta wannan

'Yan Arewa za su amfana da Amurka ta kawo tallafi mai kyau a fannoni 3 a Najeriya

Marasa lafiya sun tsere cikin firgici

Shugaban asibitin, Dakta Majid Bou'azar, ya shaida wa manema labarai cewa marasa lafiya 211 ne aka tilasta musu barin asibitin saboda hare-haren.

Ya bayyana cewa yawancinsu masu fama da cutar daji ne da ke ci gaba da samun kulawa a asibitin, wasu ma ba su iya numfshi sai da na'ura.

Wani ma'aikacin asibitin ya ce:

"Abin takaici, an yi luguden bama-bamai sosai a yankin da ke kewaye da mu. Wasu marasa lafiya na amfani da iskar oxygen da na'urorin taimakon numfashi."

"Wasu na dauke da jariransu a hannu, wasu kuma suna da allurar ruwa (IV) a hannunsu, yayin da wasu ke kan kujerun guragu. Kowa ya fito waje cikin gaggawa."

Iran ta yi Allah wadai da harin

Gwamnatin Iran ta yi kakkausar suka ga harin, tana mai zargin Amurka da aikata abin da ta kira "ta'asa" bayan da aka tilasta kwashe marasa lafiya daga asibitin.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Turawa sun shiga tashin hankali, mutane 10000 sun mutu a cikin kwana 30 kacal

"Wannan mummunan hari, wanda ya yi kama da hare-haren Isra'ila kan cibiyoyin lafiya, ya jefa yara marasa lafiya cikin tsananin firgici da wahala."
Khamenei da Trump.
Jagoran addinin kasar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Anadolu
Source: Facebook

Ya kara da cewa marasa lafiya 211 da ke karbar maganin cutar daji ne aka kwashe daga asibitin cikin gaggawa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Amurka ba ta fitar da wata sanarwa kan zargin da Iran ta yi ba, kamar yadda The Times of India ta ruwaito

Iran ta rufe mashigar Hormuz

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar IRGC ta kasar Iran sun sanar da rufe mashigar ruwa ta Hormuz har sai baba-ta-gani bayan hare-haren Amurka.

Dakarun Iran sun dauki wannan mataki ne bayan sun kai harin gargadi kan wani jirgin ruwa da suka ce ya bi hanyar ba tare da cika sharudda da samun izini ba.

Rahotanni sun ce wasu kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa Washington ta bai wa Tehran wa'adi ta dakatar da kai hare-hare kan jiragen da ke amfani da mashigin Hormuz

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262