Badakalar satar N200m: Jami’an EFCC sun yi awon gaba da akawun majalisa, matarsa da yaransa 2

Badakalar satar N200m: Jami’an EFCC sun yi awon gaba da akawun majalisa, matarsa da yaransa 2

Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC sun dira jahar Benuwe inda suka yi ram da akawun majalisar dokokin jahar, Torese Agena a kan zarginsa da hukumar take yi da satar kudi naira miliyan 200.

Mai magana da yawun hukumar EFCC reshen jahar Benuwe, Nwanyinma Okeanu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 17 ga watan Janairu ga manema labaru a garin Makurdi, babban birnin jahar.

KU KARANTA: Babban hafsan Sojan sama ya fadi matakin da Buhari ya dauka don gamawa da Boko Haram da yan bindiga

Kaakaki Okeanu yace haka zalika hukumar ta kama uwargidar akawun majalisar tare da yayansa mata guda biyu saboda kutsawa cikin ofishinsu ba bisa ka’ida ko gayyata ba, tare da cin zarafin jami’an tsaro dake gadin ofishin, amma yace sun mika su ga hukumar Yansanda.

A cewar kaakakin, a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu ne jami’an EFCC suka kama akawu Torese, kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto yana hannunsu yayin da suke cigaba da gudanar da bincike a kan zargin satar da hukumar take masa.

“Amma sai ya gayyaci matarsa da yaransa zuwa ofishin EFCC dake Makurdi inda ake rike da shi, matarsa Agena Terngu da yaransa Terfa Mamadu Ngweavese da Agena Suur sun ci zarafin yansanda biyu a bakin aiki, inda suka ciji wani dansanda a hannunsa, sa’annan suka yi kokarin take wani dansanda da mota.

“A yanzu haka Torese na hannun mu sakamakon samun izinin cigaba da rike shi da muka yi daga babbar kotun tarayya dake Makurdi, yayin da muka mika matar da yaranta biyu ga hukumar Yansanda domin ta tuhumesu tare da gurfanar da su a gaban kotu.

“Shi ma Torese Agena, akawun majalisar dokokin jahar Benuwe za mu gurfanar da shi gaban kotu da zarar mun kamma gudanar da cikakken bincike a kansa.” Inji EFCC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng