An yi kashe kashe tsakanin kabilun Tibi da Jukun a wani sabon rikici daya kaure a Taraba

An yi kashe kashe tsakanin kabilun Tibi da Jukun a wani sabon rikici daya kaure a Taraba

A yanzu haka ana cikin zaman dar dari a garin Wukari na jahar Taraba sakamakon wani sabon rikici daya kaure tsakanin mayakan kabilun Tibi da mayakan kabilun Jukun a garin a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu.

Daily Trust ta ruwaito da misalin karfe 3 na dare ne mayakan kabilun Jukun daga garin Wukari suka kaddamar da wani sabon hari a garin Jootar dake kan iyakar jahar Benuwe da jahar Taraba, amma sai kaikayi ya koma kan mashekiya, inda suka kwashi kashinsu a hannu.

KU KARANTA: Annobar Corona: Shugaban kasa ya dakatar da minista saboda karya dokar hana zirga zirga

An yi kashe kashe tsakanin kabilun Tibi da Jukun a wani sabon rikici daya kaure a Taraba

An yi kashe kashe tsakanin kabilun Tibi da Jukun a wani sabon rikici daya kaure a Taraba
Source: Facebook

Wannan rashin nasara da Jukunawa suka samu a hannun Tibabe ya lalata musu lissafi matuka, kamar yadda wani shaidan gani da ido da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar, wanda yace daga cikin wadanda harin ya shafa har da jami’in Soja da Dansanda.

Majiyar ta bayyana cewa an tura dakarun Soji da dama zuwa Takum da kuma jahar Benuwe domin kwantar da kurar da ta tashi a sakamakon yamutsin. Binciken Daily Trust ta nuna Tibabe sun kai hare hare garin Wukari har sau biyu, inda har ma matasan Jukun suka kashe guda 2 daga cikinsu.

Duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin shugaban karamar hukumar Wukari, Adigrace Daniel ya ci tura, sakamakon baya daukan kiraye kirayen da wakilinta ya yi masa ta lambar wayar salularsa.

Sai dai mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Taraba, DSP David Misal ya bayyana cewa ba zai ce uffan game da harin ba sakamakon a jahar Benuwe aka kai ba Taraba ba, amma yace Wukari na cikin lafiya.

Shi ma kwamandan Birget ta 93 dake Takum, Laftanar Kanal I Sule yace ba zai yi magana game da harin ba har sai ya tuntubi hafsoshin Soja na gaba da shi sun bashi umarni kafin yace wani abu.

A wani labarin kuma, Allah Ya kubutar da babban mashawarcin gwamnan jahar Nassarawa Abdullahi Sule a kan harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya, John Mamman, daga hannun miyagu yan bindiga da suka yi awon gaba da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel