Wata Sabuwa: INEC Na Shirin Yin Zaben Gwaji kafin Siyasar 2027 a Najeriya

Wata Sabuwa: INEC Na Shirin Yin Zaben Gwaji kafin Siyasar 2027 a Najeriya

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) na tunanin gudanar da cikakken bincike kan na'urorin zabenta da kuma gwajin zaben shugaban ƙasa
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen tabbatar da ingancin na'urorin zabe kafin 2027
  • INEC ta ce wannan shiri ya biyo bayan ƙorafi da damuwar da aka samu a zaɓen shekarar 2023 game da amincin na'urorin fasaha na zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tana duba yiwuwar gudanar da cikakken bincike a kan na'urorin fasahar zaɓenta, gami da shirya zaben gwaji domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da ya karɓi bakuncin jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery, a helkwatar INEC da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Bauchi: Tsohon kwamishina ya zama mataimakin dan takarar gwamna a APC

Shugaban hukumar zabe ta kasa
Shugaban INEC a Najeriya, Farfesa Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

INEC ta wallafa a Facebook cewa Amupitan ya bayyana cewa waɗannan shawarwari da hukumar ke nazari a kai sun samo asali ne sakamakon ƙorafin da aka samu a babban zaɓen 2023..

Gwajin na'urorin BVAS da IReV

A cewar shugaban na INEC, duba yiwuwar yin wannan bincike da kuma gwajin zaɓen zai ba su damar auna shirye-shiryensu da kuma duba ingancin na'urorinsu tun kafin ainihin ranar zaɓen.

Ya ƙara da cewa ko da yake ba a saka kuɗin gudanar da waɗannan ayyuka a cikin kasafin kuɗin hukumar na asali ba, INEC za ta nemo hanyoyin aiwatar da su saboda muhimmancinsu wajen ƙara tabbatar da sahihancin zaɓuka.

Wannan shiri na ɗaya daga cikin manyan ƙoƙarin INEC na inganta fasahar zaɓe, ciki har da ci gaba da amfani da na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a ta BVAS da dandalin nuna sakamako na IReV, tare da inganta tsarin tsaron yanar gizo na hukumar.

Kara karanta wannan

INEC ta sanya karin kudi cikin abubuwan da take bukata kafin zaben 2027

Masu kada kuri'a a Najeriya
Yadda jami'an INEC suka yi aiki a zaben Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Haɗin gwiwa da ƙasashen waje

Hukumar INEC ta bayyana cewa tana da niyyar magance duk wani kuskure ko giɓi da aka gano a zaɓukan baya kafin shekarar 2027 ta cika.

Shugaban ya bayyana fannin fasahar zaɓe da tsaron yanar gizo a matsayin muhimman wuraren da ke buƙatar haɗin gwiwa tsakanin INEC da Birtaniya da sauran abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.

A nasa ɓangaren, Montgomery ya ce ƙasar Birtaniya tana sanya ido sosai kan yadda INEC ke gudanar da shirye-shiryenta, inda ya yaba da irin haɗin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen biyu wajen dorewar dimokiraɗiyya.

Kotu ta mayar da jadawalin zabe

A wani labarin mai alaƙa da wannan, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zama a Abuja ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ya rushe jadawalin zaben 2027 da hukumar INEC ta fitar.

Kara karanta wannan

A karshe, INEC ta yi matsaya kan takarar Atiku da 'yan ADC a 2027

A cikin yanke hukunci na haɗin gwiwa da alkalan kotun guda uku suka yi, sun bayyana cewa ƙaramar kotun ta yi kuskure wajen rashin bin shari'o'in da suka riga suka zama doka.

Kotun ta ce sabon jadawalin da INEC ta fitar yana da cikakken ikon doka a ƙarƙashin Dokar Zaɓe ta 2026, don haka hukumar tana da ikon tsara ranakun gudanar da zaɓuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng