Atiku Abubakar
Wani Malamin coci a Anambra yace Jam’iyyar APC za ta doke PDP. Babban Shehin Malami ya dubo Jam’iyyar da za ta ci zaben 2019 amma za a iya rigima. Faston yace duk da shi rikakken ‘Dan PDP ne, amma APC za ta ci zabe.
Farfesa Osinbajo ya sake yin kaca-kaca da Atiku wanda shi ne dan takarar babban jam’iyyar hamayya na PDP game da batun yi wa Najeriya garambawul. Ba yau ne karon farko da Osinbajo ya soki Atiku kan batun sauya fasalin kasa.
Uwargidar Marigayi Aguiyi-Ironsi tayi magana game da zaben da za a buga a 2019. Madam Victoria Aguiyi-Ironsi tace za tayi kokarin ganin PDP tayi nasara a Abia. Iyalin na Aguyi-Ironsi za tayi wa PDP da Atiku aiki da karfin ta.`
Mun ji cewa 'Dan takarar shugabar kasa Alhaji Atiku Abubakar ya nemi Jami’an Gwamnati su binciki Surukin Shugaban kasa. A cewar sa, Junaid Abdullahi yana amfani da dukiyar Gwamnati wajen taya Buhari yakin neman zabe.
Labari ya zo mana cewa Shugaban Matasan da ke yi wa Atiku kamfe a Kano yayi murabus. Matashin yace ya ajiye mukamin ne saboda wasu dalilai da bai iya bayyanawa Duniya su ba inda yace yana mai yi wa kungiyar fatan alheri.
A jiya PDP tayi taro a Minna inda tayi alkawarin samawa Matasa da Mata aikin yi a Najeriya. Atiku yace Buhari yayi sanadin rasa aikin mutane miliyan 10. Saraki, Umaru Nasko, Tanimu Turaki, da Kwankwaso sun halarci wannan taro.
Wani Malamin addinin musulunci ya bayyana wanda zai lashe zaben 2019. Babban Limamin na Shafaudeen in Islam worldwide yace PDP za ta ba Atiku kunya. Shehin Malamin ya gargadi masu neman tada fitina su da su tuba.
Bukola Saraki yace Gwamnatin APC ta gaza kawo gyara. Saraki ya roki mutane su guji zaben Buhari a 2019 domin kuwa PDP ce za ta iya maganin talaucin da jama’a su ka shiga yace ya kamata ayi waje da Buhari a 2019.
Mun samu labari cewa jirgin yakin neman zaben Atiku zai shiga Arewa maso Gabas a gobe Talata. Bayan nan kuma mun ji labari cewa wasu kusoshi a PDP sun gayyato wani tsohon Shugaban babban bankin Amurka domin taya su kamfe.
Atiku Abubakar
Samu kari