Nafiu Bala Ya Kara Dagula Lissafin Atiku a 2027, Ya Ce Ya Zama Shugaban ADC
- Nafiu Bala Gombe ya rubuta wa hukumar INEC wasika, yana sanar da ita cewa ya koma kan mukaminsa na shugaban jam’iyyar ADC na kasa
- Ya bukaci hukumar ta amince da shi a matsayin shugaban jam’iyyar tare da sabunta bayanan ADC da ke shafinta na intanet
- Wannan na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar karkashin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Nafiu Bala Gombe ya sanar da hukumar INEC cewa ya koma kan mukaminsa na shugaban jam’iyyar ADC na kasa, bisa hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja.
A wasikar da ya aike wa shugaban INEC ranar 16 ga Nuwamba, 2026, Gombe ya bukaci hukumar ta amince da shi a matsayin shugaban ADC domin dukkan harkokin hukuma, wasiku da takardun jam’iyyar.

Source: Twitter
A sakon da ya wallafa a Facebook, Nafi Bala ya danganta matakin nasa da hukuncin da Mai shari’a Peter Lifu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar 5 ga Nuwamba, 2026.
An bukaci INEC ta sabunta bayanan ADC
A cikin wasikar mai lamba ADC/NHQ/CH/2026/001, Gombe ya ce ya koma bakin aikinsa ne bisa hukuncin kotu a karar da ya shigar kan ADC da wasu mutane hudu.
Ya bukaci INEC ta amince da shi a matsayin shugaban jam’iyyar, tare da sabunta bayanan ADC da ke shafinta na intanet domin nuna matsayinsa.
Gombe ya kuma ce ya hada kwafin hukuncin kotun da aka tabbatar da sahihancinsa domin hukumar ta yi amfani da shi wajen daukar matakin da ya dace.
Ya tabbatar wa INEC cewa zai mutunta tsarin mulkin jam’iyyar, bin doka da ka’ida, tare da samar da kyakkyawar alaka da hukumar domin ci gaban dimokuradiyya.
Hukuncin da kotu ta yanke
A ranar 5 ga Nuwamba, 2026, Mai shari’a Peter Lifu ya soke shugabancin jam’iyyar karkashin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da kuma matakan da kwamitin ya dauka.
Sai dai bayanan hukuncin da jaridar Punch ta wallafa sun nuna cewa kotun ba ta ayyana Gombe a matsayin shugaban jam’iyyar na dindindin kai tsaye ba.

Source: Twitter
A maimakon haka, ta bayyana shi a matsayin kadai zababben mamba na kwamitin gudanarwa na kasa da wa’adinsa bai kare ba, wanda INEC za ta amince da shi wajen kula da harkokin jam’iyyar.
Hukuncin ya kuma jefa ayyana Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027 cikin takaddama, sakamakon soke matakan da suka kai ga fitowarsa takara.
Amaechi ya ce Atiku zai yi nasara
A wani labarin, kun ji cewa mataimakin dan takarar shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsu na samun goyon bayan jihohi 13 a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma gabanin zaben 2027.
Amaechi ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa ADC za ta kalubalanci Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, tare da cewa tana kuma kokarin samun goyon baya a Kudu maso Kudu da Arewa ta Tsakiya.
A wani gangamin yakin neman zaben ADC da aka gudanar a jihar Bauchi, ya yi hasashen cewa jam’iyyar za ta samu nasara a jihohin Neja, Kogi da Nasarawa.
Asali: Legit.ng

