ADC Ta Gamu da Cikas, Kotu Ta Kori Mutumin Atiku da ke Takarar Gwamna
- Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tsige Tukur Ribadu daga matsayin ɗan takarar gwamnan Adamawa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027
- Kotun ta umarci INEC da ta dawo da sunan Ambasada Omar Suleiman a matsayin halastaccen ɗan takarar jam’iyyar
- Mai shari’a ya ce ba za a iya sauya sunan Suleiman ba sai ya mutu ko kuma ya janye takararsa da kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tsige Tukur Ribadu daga matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.
Kotun ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta dawo da sunan Ambasada Omar Suleiman a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar.

Source: Facebook
Ɗan uwan Babachir ya yi nasara a kotu
Suleiman, wanda ɗan uwan tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ne, shi ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ADC a Adamawa, cewar Vanguard.
Sai dai daga baya jam’iyyar ta sauya shi da Tukur Ribadu, wanda rahoton ya bayyana a matsayin mutumin da ke da kusanci da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Suleiman ya garzaya kotu kan sauya shi
Bayan sauya sunansa, Ambasada Omar Suleiman ya garzaya kotu domin ƙalubalantar matakin da jam’iyyar ta ɗauka na cire shi daga takarar gwamnan jihar Adamawa.
A hukuncin da ta yanke, kotun ta bayyana cewa ba za a iya sauya sunan Suleiman a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ba, matuƙar bai janye takararsa da kansa ba ko kuma ya rasu.
Kotun ta ce tun da Suleiman bai janye daga takarar ba kuma yana raye, matakin sauya shi da wani ɗan takara ya saɓa wa doka, don haka ba shi da inganci.
Kotun ta umarci INEC ta dawo da sunan Suleiman
Saboda haka, kotun ta umarci hukumar INEC da ta gaggauta dawo da sunan Ambasada Omar Suleiman a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam’iyyar ADC.
Hukuncin na zuwa ne yayin da rikicin cikin gida kan wanda zai wakilci jam’iyyar ADC a zaɓen gwamnan Adamawa na 2027 ke ci gaba da ɗaukar sabon salo.
Yadda aka dakatar da Atiku, Babachir
Wani tsagi na ADC a jihar Adamawa ƙarƙashin Raji Zumo ya yi taron sanar da dakatar da Atiku Abubakar da wasu mutane biyu daga jam'iyyar.
Raji Zumo ya zargi Atiku da sauran mutanen da hannu wajen ƙirƙirar rassan bogi a jam'iyyar, raunana tsarin shugabanci, da yin watsi da umarnin kotu.
ADC ta musanta sauya dan takara
A wani labarin, an ji cewa jam'iyyar ADC a Adamawa ta yi martani kan rahotannin da suke yawo game da maye gurbin ɗan takararta, Ambasada Injiniya Umar Suleiman.
Jam'iyyar ta ce Umar Suleiman ne halastaccen ɗan takara, babu batun janye takara, maye gurbinsa ko wata tattaunawar sauya sunansa.
ADC ta ce shugabannin ƙananan hukumomi 21 sun tabbatar da goyon bayansu gare shi, tare da roƙon al'umma su yi watsi da jita-jita.'
Asali: Legit.ng

