Ku daina ruduwa da masu neman batawa Miji na suna - Matar Atiku ta fadawa Matan Kudu

Ku daina ruduwa da masu neman batawa Miji na suna - Matar Atiku ta fadawa Matan Kudu

Daya daga cikin masu dakin ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar mai suna Dr. Jennifer Douglas Abubakar tayi kira ga jama’an kasar nan da cewa ka da su rudu da sharrin da ake yawan yi wa Mai gidan ta.

Ku daina ruduwa da masu neman batawa Miji na suna - Matar Atiku ta fadawa Matan Kudu
Matar Atiku ta fadawa Mutanen Najeriya su zabi PDP a 2019
Asali: UGC

Dr. Jennifer Douglas Abubakar ta bayyana cewa akwai masu neman batawa Alhaji Atiku Abubakar suna da karfi da yaji domin ganin bai kai labari a zaben bana. Misis Douglas Abubakar tace Atiku yana da niyyar gyara kasar nan.

Jennifer Abubakar ta zanta da Matan Kudancin Najeriya a wani taro da jam’iyyar PDP ta shirya jiya Ranar Litinin a Garin Benin da ke cikin Jihar Edo. Wannan Baiwar Allah ta zayyano irin manufofin Atiku idan ya samu mulki.

KU KARANTA: Buhari ya fara kokarin jawo Matasa da tayin kujerun Ministoci

Matar ‘dan takarar tace Atiku zai inganta tsaro da kuma gyara harkar tsaro tare da inganta kiwon lafiya idan jama’a su ka zabe sa a matsayin shugaban kasa. Daya daga cikin Matar ‘dan takarar ta ba ‘yan uwan ta wannan tabbaci jiya.

Jenifer wanda asalin Baturiya ce ta nemi jama’a musamman mata da matasa su marawa Atiku Abubakar baya, wanda a cewar ta shi ne ya fi cancanta a zaben da za ayi bana idan har ana neman ‘dan takarar da zai gyara Najeriya.

Kwanan nan ne kuma wata daga cikin Matan ‘dan takarar na PDP, Atiku Abubakar, ta kawo ziyara zuwa Arewacin Najeriya inda ta ziyarci tsohon gwamnan Jigawa kuma jigo a PDP watau Alhaji Sule Lamido.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng