Cikin Hotuna: Atiku ya gudanar da taron yakin neman zabe a jihar Taraba

Cikin Hotuna: Atiku ya gudanar da taron yakin neman zabe a jihar Taraba

Mun samu cewa, a jiya Talata, 5 ga watan Fabrairu, jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin kasar nan ta cika ta batse yayin gudanar da taron yakin neman zabe na dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa tare da tawagar sa ta jiga-jigan jam'iyyar PDP sun samu kyakkyawar tarba ta shugabanni da kuma magoya baya a jiya Talata yayin saukar su a filin jirgin sama na Danbaba Suntai da ke jihar Taraba domin gudanar da taron yakin neman zabe.

Gwamnan jihar Taraba; Ishaku Darius yayin fasa taro a yakin neman zaben Atiku

Gwamnan jihar Taraba; Ishaku Darius yayin fasa taro a yakin neman zaben Atiku
Source: Twitter

Gwamnan jihar Taraba; Ishaku Darius yayin daga tutar sa a taro a yakin neman zaben Atiku

Gwamnan jihar Taraba; Ishaku Darius yayin daga tutar sa a taro a yakin neman zaben Atiku
Source: Twitter

Jihar Taraba ta cika ta batse yayin taron yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP

Jihar Taraba ta cika ta batse yayin taron yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP
Source: Twitter

Al'umma sun shaida yayin taron yakin zaben Atiku a Taraba

Al'umma sun shaida yayin taron yakin zaben Atiku a Taraba
Source: Twitter

Atiku ya fasa taro yayin gudanar da taron sa na yakin neman zabe a jihar Taraba

Atiku ya fasa taro yayin gudanar da taron sa na yakin neman zabe a jihar Taraba
Source: Twitter

Shugaban PDP na kasa yayin gabatar da jawaban sa a Taraba

Shugaban PDP na kasa yayin gabatar da jawaban sa a Taraba
Source: Twitter

Atiku da jiga-jigan PDP a taron sa na yakin neman zabe cikin birnin Jalingo

Atiku da jiga-jigan PDP a taron sa na yakin neman zabe cikin birnin Jalingo
Source: Twitter

Atiku ya samu karbuwa yayin taron sa na yakin neman zabe cikin birnin Jalingo

Atiku ya samu karbuwa yayin taron sa na yakin neman zabe cikin birnin Jalingo
Source: Twitter

Jihar Taraba ta cika ta batse ya amsa amo na goyon bayan Atiku

Jihar Taraba ta cika ta batse ya amsa amo na goyon bayan Atiku
Source: Twitter

Jihar Taraba ta tumbatsa yayin taron yakin neman zaben Atiku

Jihar Taraba ta tumbatsa yayin taron yakin neman zaben Atiku
Source: Twitter

Da yake gabatar da jawaban sa yayin taron yakin neman zabe a jihar Taraba, Wazirin Adamawa ya sha alwashin kawo karshen rashin tsaro musamman ta'addanci a yankin Arewa maso Gabas muddin ya yi nasara yayin babban zaben kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Kazalika tsohon mataimakin shugaban kasar ya sha alwashin kammala katafaren aikin samar da wutar lantarki na Mambilla cikin kankanin lokacin yayin samun nasarar tare da shimfida tsare-tsare na habaka da inganta tattalin arzikin kasar nan.

KARANTA KUMA: Babban Sufeton 'yan sanda ya ziyarci shugaban kamfanin man fetur na kasa, Maikanti Baru

Cikin jawaban sa yayin taron yakin zaben da aka gudanar cikin babban birni na Jalingo, Atiku ya yi kira tare da jan hankalin hukumomin tsaro wajen kauracewa shiga harkokin siyasa ta hanyar sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya rataya a wuyan su.

Yayin da al'ummar Najeriya ke ci gaba da hankoro gami da muradin samun ingataccen tsaro, ayyukan yi da inganta jin dadin rayuwar su cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, gwamnan jihar Taraba Ishaku Darius ya ce ba bu wani mafificin zabi da zai tabbatar da cikar wannan buri face Atiku.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel