Da Atiku da gaske yake yi da ya sakewa Najeriya fasali lokacin yana mulki - Osinbajo
Daily Trust ta rahoto cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya kuma caccakar ‘dan takarar babban jam’iyyar hamayya na PDP watau Alhaji Atiku Abubakar game da batun yi wa tsarin Najeriya garambawul.

Asali: Depositphotos
Mataimakin shugaban kasa watau Yemi Osinbajo ya sake jadadda cewa Atiku Abubakar yana cikin wadanda su ka hana ayi wa tsarin Najeriya kwaskwarima a lokacin yana rike da kujerar mataimakin shugaban kasa a 1999.
Farfesa Osinbajo yayi wannan jawabi ne a wajen taya Bisi Akande, murnar cika shekaru 80 a Duniya a tsakiyar makon nan. Cif Bisi Akande yana cikin wadanda su kayi sanadiyyar kafa jam’iyyar APC a Najeriya a shekarar 2013.
KU KARANTA: Dalilin da yasa nake neman in zarce a kan mulki – Shugaba Buhari
Yemi Osinbajo ya bayyana cewa tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi bakin kokarin sa wajen ganin an karawa jihohi karfi a lokacin gwamnatin Obasanjo amma irin su Atiku su ka murtuke fuska su ka hana ayi hakan.
Osinbajo yace yunkurin ragewa gwamnatin tarayya karfi yana cikin abin da su ka fara tattaunawa da Bola Tinubu a 1999 wanda har ya sa su ka shiga har kotun koli da gwamnatin Najeriya fiye da sau 12 a lokacin mulkin Obasanjo da Atiku.
Sai dai kuma yanzu tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yana kiran cewa zai sakewa Najeriya fasali idan ya samu mulki, wanda Yemi Osinbajo yake ganin cewa akwai alamun yaudara a lamarin ‘dan takarar jam’iyyar PDP.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng