Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake lashe zaben 2019 – Olagoke
- Wani Malamin addini, Sabit Olagoke yace Buhari ne zai ci zaben 2019
- Babban Limamin yace Jam’iyyar PDP za ta ba Atiku Abubakar kunya
- Malamin ya kuma gargadi masu neman tada fitina su da su sake tunani
Babban Limamin Shafaudeen Islam watau Sabit Olagoke ya fito ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar nan, Alhaji Atiku Abubakar, ba zai yi nasara a zaben 2019 ba. Olagoke yace jam’iyyar PDP ce za ta ba Atiku kunya a zaben na badi.
Sheikh Sabit Olagoke wanda yana cikin Malaman da ake ji da shi a Kasar Yarbawa yake cewa duk da karfin Atiku Abubakar, Buhari ne zai koma kan karagar mulki a 2019. Malamin ya kuma bayyana abubuwa da dama da za su faru a shekarar 2019.
KU KARANTA: Atiku na kulle-kullen shigowa da makudan kudi domin zaben 2019
Farfesa Sabit Olagoke ya kuma kara da cewa, wasu mutane su na da shirin tada fitina a zaben 2019. Shehin yace duk masu wannan mugun nufi, ba za su kwana lafiya ba. Fitaccen Malamin yayi duk wannan jawabi ne a Garin Ibadan, a Jihar Oyo.
Olagoke ya kuma yi magana game da sha’anin tsaro a Najeriya, inda yace sai an kara dagewa da addu’a a 2019. Malamin ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya da kuma harkar ilmi zai bunkasa a 2019. Malamin yace za a cigaba har a harkar wasanni.
Farfesan wanda ya taba rike mukami a wata babbar Makaranta da ke Garin Ilaro a Jihar Ogun ya koka da irin kudin da ake warewa harkar ilmi a kasafin Najeriya. Farfesan yace abin da ake batarwa yayi kadan idan aka duba sharudan Hukumar UNESCO.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng