Idan ana son fita daga wahalar da APC su ka jefa jama’a, a zabi Atiku - Saraki

Idan ana son fita daga wahalar da APC su ka jefa jama’a, a zabi Atiku - Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya koka da halin rashin tsaro da kuma kangin talauci da jama’a su ka shiga a Najeriya a karkashin mulkin gwamnatin APC da ke ci a halin yanzu.

Idan ana son fita daga wahalar da APC su ka jefa jama’a, a zabi Atiku - Saraki

Saraki yace Gwamnatin APC ta gaza kawo gyara a fannin tsaro da tattali
Source: UGC

Dr. Bukola Saraki ya bayyana cewa ba a taba samun lokacin da aka jefa al’umma cikin matsanancin wahalar kamar lokacin gwamnatin nan mai ci ba. Saraki y aba jama’an kasar musamman mutanen Kwara hakuri na halin da su ke ciki.

Saraki yayi wannan jawabi ne lokacin da ya aikawa mutane sakon sa na bikin kirismeti a gidajen rediyon a Kwara. Saraki wanda yanzu haka yana Garin Ilorin yayi magana a tashar Harmony FM, Idofian, Royal FM, Sobi FM da Gidan Rediyo Kwara.

KU KARANTA: Ana zargin Surukin Buhari da ke rike Hukumar BDCA da aikata ba dai-dai ba

Shugaban majalisar kasar yace muddin mutane su na so su ka ga an samu gyara ta fuskar tattalin arziki da sha’anin tsaro, dole a zabi Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a zaben 2019. Saraki yace Atiku ne zai iya gyara tattalin arzikin Najeriya idan ya samu mulki.

Sanatan yake cewa a 2015, yayi alkawarin cewa APC za tayi maganin talauci da rashin aikin yi da kuma sha’anin tsaron kasa, bayan ganin abubuwa sun kuma jagwalgwalewa na Saraki yace ya fice daga APC domin gwamnatin ta ta gaza kawo wani gyaran kirki.

Dr. Saraki ya roki mutane su guji zaben Buhari a 2019 domin kuwa PDP ce za ta iya maganin talaucin da aka shiga. Haka kuma Saraki ya nuna godiya ga Allah da ya rike majalisar dattawa inda yace yayi amfani da wannan dama wajen yi wa mutanen sa aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel