Hadimin Tinubu Ya Fadi Jihohi 2 da APC Za Ta Iya Shan Kaye a Zaben Shugaban Kasa na 2027

Hadimin Tinubu Ya Fadi Jihohi 2 da APC Za Ta Iya Shan Kaye a Zaben Shugaban Kasa na 2027

  • Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce APC na da damar lashe jihohi uku a yankin Kudu maso Gabas a zaɓen 2027
  • Ya amince cewa Peter Obi na da karɓuwa sosai a Abia da Anambra, inda APC za ta iya fuskantar ƙalubale da rashin nasara
  • Mai taimaka wa Tinubu kan sadarwa ya ce yana ganin ’yan adawa ba su shirya tunkarar APC a babban zabe mai zuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan sadarwa da dabaru, Daniel Bwala, ya yi hasashen jihohin da APC za ta iya shan kaye a zaben 2027.

Bawala ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta lashe jihohi uku a yankin Kudu maso Gabas a babban zaɓen 2027, sannan ya amince cewa Peter Obi na iya ci gaba da samun galab a Abia da Anambra.

Kara karanta wannan

Abba ya yi wa Kwankwaso tonon silili kan shiga APC da zuwa wajen Tinubu

Daniel Bwala.
Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan sadarwa da dabaru, Daniel Bwala Hoto: Daniel Bwala
Source: Facebook

Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Morning Brief na gidan talabijin na Channels Television a ranar Litinin, inda aka tambaye shi yadda jam’iyya mai mulki ke shirin samun nasara a yankin.

Ya ce karɓuwar Obi a jihohin biyu na iya sa APC ta sha wahala wajen samun nasara a can, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta lashe sauran jihohin Kudu maso Gabas.

“Za mu sha wahala a Abia. Ka ga, a Abia da Anambra, Peter yana da karfi sosai. Ko a waɗannan jihohi biyu, ina hasashen cewa ko da mun sha kashi, za mu zo na biyu, wanda ba abu ne mara kyau ba.
"Amma ban da waɗannan jihohi biyu, sauran jihohin za mu lashe su,” in ji Bwala.

Sai dai mai taimaka wa shugaban ƙasar ya jaddada cewa hasashen da ya yi ba tabbataccen sakamako ba ne, illa hasashe kawai.

Kara karanta wannan

Abin da matasa suka yi wa Dauda Kahutu Rarara a masallacin Abuja ya fusata jigon APC

Ya lura cewa ’yan siyasa daban-daban na iya fassara bayanan da suke da su ta hanyoyi mabambanta, su kuma yi hasashe daban-daban.

Ya ce jam’iyyar APC a shirye take ta amince da wuraren da za ta iya fuskantar matsaloli, maimakon yin ikirarin cewa za ta lashe dukkan jihohin yankin.

“Akwai Inda muke ganin ba za mu iya ba, kuma ina amfani da wannan kalma ne da taka-tsantsan, domin babu wani abu cikin abin da nake faɗa da aka tabbatar ba zai sauya ba.
"Hasashe ne kawai, kuma mutum biyu daga jam’iyya ɗaya za su iya yin hasashe daban-daban bisa yadda kowannensu ya fassara bayanan da yake da su,” in ji shi.

Bwala ya ƙara da cewa amincewa da yiwuwar fuskantar shan kaye a wasu wurare ya fi gaskiya fiye da ikirarin cewa APC za ta lashe ko’ina. Ya ce amfani da kalmar “sha wahala” yana nufin yiwuwar jam’iyyar ta kasa lashe waɗannan jihohi ne kawai.

Haka kuma, mai ba shugaban ƙasa shawarar ya nuna kwarin gwiwa kan damar APC na samun nasara a babban zaɓen 2027, inda ya yi watsi da shirye-shiryen ’yan adawa na ƙalubalantar jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

“Ba na ganin ’yan adawa sun shirya. Waɗanda suka fahimci yadda siyasa ke tafiya za su iya ganin cewa tuni suna fuskantar shan kashi,” in ji shi.

Tinubu ya ja hankalin 'yan Najeriya

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su tantance gwamnatinsa bisa ayyukan da ta gudanar, ba alkawuran siyasa ba a zaben 2027.

Ya kuma ƙalubalanci abokan hamayyarsa na siyasa da su bayyana abin da suka yi lokacin da suke riƙe da muƙaman gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262