Hadimin Gwamna Ya Yi Magana Ta Adalci kan Abin da Ya Faru tsakanin Sarkin Daura da Baturiya
- Ossai Ovie Success ya ce ya kamata Mirka Czee ta sanya iyaka yayin ganawarta da Sarkin Daura, bayan zargin cin zarafin da ta yi masa
- Ya tambayi dalilin da ya sa matar ta zauna kusa da sarkin, sannan ta ci gaba da zama a ɗakin bayan zargin taɓa hannunta da ya yi
- Czee ta zargi Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, da rungumarta, sumbatar kumatunta da kuma taɓa ƙirjinta ba tare da izininta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Delta - Ossai Ovie Success, mai taimaka wa Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya ce ya kamata 'yar yawon buɗe ido daga Poland, Mirka Czee, ta sanya iyaka yayin ganawarta da Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk.
Hadimin gwamnan ya ce bai kamata a ɗora wa basaraken laifi shi kaɗai ba tare da duba yadda matar ta gudanar da kanta yayin ziyarar ba.

Kara karanta wannan
Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da matar da ake zargin Sarkin Daura ya taɓa jikinta

Source: Instagram
Ossai ya bayyana ra'ayinsa ne a wani saƙo da ya wallafa a Facebook ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamban 2026.
Abin da hadimin gwamnan ya ce
A cikin saƙonsa, Ossai ya ce kafin a zargi Sarkin Daura, ya kamata a yi la'akari da yadda abubuwa suka gudana a lokacin ganawar.
Ossai ya tambayi dalilin da ya sa Czee ta zauna kusa da sarkin a karon farko da suka haɗu, maimakon ta zauna a ɗayan gefen kujera.
Ya bayyana hakan a matsayin abin da ya shafi hankali da sanin iyakokin mu'amala tsakanin mutane.
Ossai ya kuma soki yadda matar ta ci gaba da zama a ɗakin bayan zargin da ta yi cewa sarkin ya riƙe hannunta yana shafa shi.
A cewarsa, da zarar hakan ta faru, ya kamata ta ja da baya, ta nuna rashin amincewarta sannan ta kawo ƙarshen ganawar.
"A lokacin da aka riƙe hannunta aka fara shafa shi ba yadda ya kamata ba, wannan shi ne lokacin da ya kamata ta nuna iyaka sosai, ta ja hannunta baya sannan ta dakatar da ganawar nan take.” In ji shi.

Kara karanta wannan
"Tikitina ya fi na Obi da Kwankwaso"; Dan takarar shugaban kasa ya kawo dalilinsa
Ya ce ba ya kare Sarkin Daura
Duk da sukar da ya yi wa Czee, Ossai ya jaddada cewa ba ya kare Sarkin Daura ko halin da ake zarginsa da aikatawa. Ya ce ya kamata shugaba ya san yadda zai mutunta mutane tare da kare martabarsa.
“Babu wanda ke kare munanan halaye daga kowa. Ya kamata shugaba ya fi kowa sanin abin da ya dace, tare da kare martabarsa.
“Dole ne shugabanni su mutunta iyakokin mu'amala. Baƙi kuma dole ne su sanya nasu iyakokin. Na ji takaici.” In ji shi.
Yadda zargin cin zarafin ya fara
Maganganun Ossai sun biyo bayan yaɗuwar wani bidiyo da Czee ta ɗauka yayin ziyararta fadar Sarkin Daura da ke jihar Katsina.
Matar, wadda aka haifa a Jamhuriyar Czech, ta zargi sarkin da cin zarafinta ta hanyar taɓa jikinta ba tare da izininta ba.
A cewarta, sarkin ya nemi ta zauna kusa da shi, sannan ya riƙe hannunta yana wasa da shi. Ta kuma yi zargin cewa ya rungume ta, ya sumbaci kumatunta, sannan ya taɓa ƙirjinta ba tare da izininta ba.

Source: Facebook
An bukaci a binciki Sarkin Daura
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International reshen Najeriya ta bukaci gwamnatin jihar Katsina da rundunar ’yan sanda su binciki Sarkin Daura.
Kungiyar ta bukaci hakan ne biyo bayan zargin cin zarafin wata mata yar yawon bude ido da aka alakanta da Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk.
Asali: Legit.ng