Rikakken Malamin coci a Anambra ya ba Shugaba Buhari nasara a zaben 2019
Mun ji labari cewa wani Malamin addinin kirista wanda yayi kaurin-suna ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta Shugaba Muhammadu Buhari ce ta za tayi nasara a babban zaben da za ayi a bana.

Asali: Depositphotos
Kamar yadda mu ka ji labari daga jaridar Pulse ta kasar nan, Dr Ramas Azuzu, ya gano cewa APC ce za ta sake lashe zaben 2019. A harsashen wannan babban malamin, Buhari zai doke Abokan hamayyar sa irin su Atiku Abubakar.
Babban Faston kuma Jagoran cocin nan na Liberation Temple of the Absolute God, ya bayyana wannan ne lokacin da yake magana da wasu ‘yan jarida a Ranar Lahadin nan da ta gabata a cikin garin Anaocha da ke jihar Anambra.
KU KARANTA: An bankado wata makarkashiyar Boko Harm daf da zaben 2019
Shehin Malamin ya kuma bayyanawa jama’a cewa akwai yiwuwar rikici ya barke bayan zaben don haka yayi kira a yawaita addu’o'i. Wannan malami na kirista dai yace da yayi na sa duban, an nuna masa cewa Buhari ne zai ci zabe.
Babban Faston ya kuma yabawa gwamnatin Buhari wanda a cewar sa, ta ceci kasar nan daga halin ha’ula’i. Wannan babban Malami yace yana cikin wadanda su ka fara nunawa Goodluck Jonathan cewa zai iya fadi zabe tun kafin 2015.
Ramas Azuzu yace shugaba Muhammadu Buhari yayi kokarin wajen maganin cin hanci da satar dukiyar gwamnati a Najeriya. Faston yace duk da shi rikakken ‘Dan PDP ne, amma an nuna masa cewa Buhari ne zai lashe zaben bana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng