Babbar Magana: Ana Zargi Wasu Mutane Sun Shirya Sace Kwamishina da Iyalinsa
- Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kebbi, Yakubu Ahmed-BK, ya kai ƙorafi wurin DSS kan zargin yunƙurin sace shi da iyalansa
- Ya ce wata mota ƙirar van mai launin fari da gilashinta ke da duhu ta yi ƙoƙarin kusantarsu yayin da shi da matarsa ke motsa jiki da safe
- Ya nemi a gudanar da bincike cikin gaggawa tare da samar da tsaro ga iyalansa da sa ido kan motar da ake zargi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kebbi, Yakubu Ahmed-BK, ya yi zargin wasu mutane da ba a sansu ba sun yi yunkurin yin garkuwa da shi da iyalinsa.
Bisa haka, ya kai rahoto ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) kan zargin yunƙurin sace shi da wasu ’yan uwansa a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa korafin, wadda aka rubuta ranar 15 ga Nuwamban 2026, an miƙa shi ne ga shugaban DSS ta hannun Mataimakinsa mai kula da ayyuka.
An kuma aika kwafin ƙarar ga Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi.
A cikin wasiƙar, kwamishinan ya buƙaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan abubuwan da ya ce sun faru.
Abin da ya faru da kwamishinan Kebbi
A cewar takardar, lamarin farko ya faru ne a ranar 10 ga Nuwamba, 2036 lokacin da shi da matarsa suka fita yin motsa jiki kamar yadda suka saba da sassafe a kan titin Sani Abacha Bypass.
Kwamishinan ya yi zargin cewa wata mota ƙirar van mai launin fari, wadda aka yi wa gilashinta duhu sosai, ta zo ne tana tafiya a kan titin ba bisa hanyar da ya kamata ba. Motar tana da lambar rajista mai launin ja ta Agege.

Kara karanta wannan
Abin da matasa suka yi wa Dauda Kahutu Rarara a masallacin Abuja ya fusata jigon APC
Ya ce motar ta rage gudu a gefensu, sannan ta yi kamar wani daga cikin waɗanda ke cikinta zai buɗe ƙofar motar. Ya kuma bayyana cewa ya hango wani abu da ya yi kama da bakin bindiga.
Ahmed-BK ya ce shi da matarsa sun yi gudu zuwa wani babban ginin shaguna da ke kusa domin neman mafaka, bayan sun fara zargin cewa mutanen da ke cikin motar suna binsu ne.
Ya bayyana cewa ya kira wani jami’in tsaro da ke aiki a gidan gwamnatin jihar domin neman agaji. Jami’in ya isa wurin jim kaɗan bayan kiran, lamarin da ya tilasta wa motar yin sauri ta bar wurin.
Kwamishinan ya kuma yi zargin cewa an sake ganin motar a kusa da gidansa na biyu da ke unguwar Bayan Oando a tsakanin ƙarfe 6:30 zuwa 7:00 na safiyar ranar 15 ga Nuwamba.
Abin da ya nema daga hukumomin tsaro
Daga cikin buƙatun da ya gabatar akwai tura jami’an tsaro sanye da tufafin farar hula na ɗan lokaci domin kare iyalansa.
Ya kuma nemi a sanya ido kan motar da ake zargi, tare da ƙara sa ido kan wasu sassan titin Sani Abacha Bypass, musamman tsakanin ƙarfe 6:00 zuwa 7:00 na safe.
Bugu da ƙari, ya buƙaci hukumomin tsaro su ɗauki matakan da suka dace domin gano mutanen da ke da hannu a yunƙurin da ake zargin an yi na cutar da shi da iyalansa.
Kwamishinan ya jaddada buƙatar gudanar da bincike cikin gaggawa domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin da kuma tabbatar da tsaron iyalansa.
Malami ya kai korafi ga yan sandan Kebbi
Kun ji cewa dan takarar gwamnan jihar Kebbi na ADC, Abubakar Malami SAN ya shigar da ƙara a gaban kwamishinan ’yan sandan jihar Kebbi kan rushe gininsa a Birnin Kebbi.
Tsohon ministan ya umarci lauyoyinsa su nemi hakkinsa ta hanyar shari’a tare da neman diyyar barnar da aka yi.
Asali: Legit.ng

