Jirgin yakin neman zaben Atiku Abubakar zai shiga Arewa maso Gabas

Jirgin yakin neman zaben Atiku Abubakar zai shiga Arewa maso Gabas

- Atiku zai shiga Arewa maso Gabashin Najeriya domin cigaba da kamfe

- Buhari yana da Mutane a Yankin duk da cewa daga nan ne Atiku ya fito

- PDP ta kuma dauko Alan Greensman domin ya taya ta yakin zabe a 2019

Jirgin yakin neman zaben Atiku Abubakar zai shiga Arewa maso Gabas

Atiku Abubakar zai yi taron babban kamfe a cikin Jihar Gombe
Source: Depositphotos

Labari ya kai gare mu cewa Jam’iyyar adawa ta PDP za ta cigaba da yawon yakin neman zaben da ta ke yi a bangarorin Najeriya. A wannan makon, Jam’iyyar hamayyar za ta soma ne da Arewa maso Gabashin kasar nan.

Sakataren yada labarai na Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya aikawa Jama’a goron gayyata na taron gangamin da PDP ta shirya a Jihar Gombe da ke cikin Gabashin Arewacin Najeriya. Za ayi taron ne gobe Ranar Talata.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari zai yi makon kudi a wajen yakin neman zaben 2019

Kamar yadda babban Jami’in na PDP ya sanar, an shirya taron kamfen din ne a filin wasan kwallon kafa da ke cikin Garin Gombe. Za a soma taron ne da karfe 10: 00 na safiyar Ranar 18 ga Watan na Disamba idan Allah ya so.

Jam’iyyar ta na gayyatar duka ‘Ya ‘yan ta wadanda su ka hada da ‘Yan Majalisu da sauran Shugabanni da masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar a matakan Jiha da kuma Tarayya wajen yakin neman zaben na Atiku Abubakar.

Wasu kusoshi a PDP sun gayyato wani tsohon Shugaban babban bankin Amurka watau Alan Greenspan domin ya taya Jam’iyyar shiryawa zaben 2019. Greenspan rikakken Masanin tattali arziki ne da aka ji da shi a Amurka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel