Rashin kafa tubalin hadin kai na jam'iyyar PDP zai sanya Atiku ya sha kasa a jihar Legas - Ogunwele

Rashin kafa tubalin hadin kai na jam'iyyar PDP zai sanya Atiku ya sha kasa a jihar Legas - Ogunwele

- Tsohon Ministan ayyuka ya gargadi jam'iyyar PDP akan rashin kafa tubalin hadin kai da zai janyo mata asara yayin babban zabe a jihar Legas

- Sanata Adeseye Ogunwele ya ce rashin hadin kan ya jam'iyyar PDP tun yayin zaben fidda gwani zai janyo mata babban kalubale yayin babban zabe.

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Legas ta musanta wannan ikirari da cewar ta kasance tamkar tsintiya madaurin ki daya

Wani babban jigo na jam'iyyar PDP kuma tsohon Ministan aikace-aikace, Sanata Adeseye Ogunwele, yayi karin haske tare da gargadi dangane da babbar barazana da jam'iyyar za ta iya fuskanta yayin babban zaben kasa a jihar Legas.

Sanata Ogunwele ya ce rashin kafa kyakkyawan tubali da kuma nagartaccen ginshiki na hadin kai a jam'iyyar PDP zai iya haddasa ma ta babbar asara yayin zaben kasa da zai gudana a watan Fabrairu da kuma watan gobe na Maris.

Tsohon Ministan ya yi wannan gargadi yayin bayyana shirye-shiryen jam'iyyar sa ta PDP dangane da zaben kujerar shugaban kasa da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu. Ogunwele ya ce rashin hadin kai ka iya haddasa ma ta faduwa wanwar yayin zaben.

Atiku yayin halartar wani taron zayyana manufofi a jihar Legas

Atiku yayin halartar wani taron zayyana manufofi a jihar Legas
Source: Twitter

Babban jigon ya bayyana damuwar sa kwarai da aniyya dangane da yadda rashin hadin kai ya tsananta a jam'iyyar reshen jihar tun yayin zaben fidda gwani da ta gudanar a karshen shekarar da ta gabata.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon Ministan na ci gaba da bayyana fargaba gami da damuwa bisa ga yiwuwar rashin samun nasarar jam'iyyar PDP a matakin kujerar gwamna da kuma na shugaban kasa yayin babban zabe.

KARANTA KUMA: Buhari ya rantsar da Farfesa Owasanoye sabon shugaban hukumar ICPC

Ya ce dole jam'iyyar ta zage dantse tare da daura damarar kafa nagartaccen tubalin hadin kai domin gujewa shan kasa a hannun jam'iyyar APC yayin zaben kujerar shugaban kasa da kuma na gwamna a jihar Legas.

Yayin musanta wannan ikirari, Dayo Williams, jagoran wata kungiyar magoya bayan dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba bu wannan zance domin kuwa a halin yanzu jam'iyyar na ci gaba da kasancewa tamkar tsintsiya madauri daya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel