Allura ta tono garma: Atiku da Obasanjo na da hannu cikin kashe tsohon ministan sharia - Soyinka

Allura ta tono garma: Atiku da Obasanjo na da hannu cikin kashe tsohon ministan sharia - Soyinka

Shahararren marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka ya nuna yatsa ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mataimakinsa, Atiku Abuabakar game da kisan tsohon ministan sharia kuma babban kauyan gwamnati a zamanin mulkinsu, Cif Bola Ige.

Soyinka ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, 6, ga watan Feburairu, inda ya tuna ma Duniya cewa a shekarar 2001 aka kashe Bola Ige, kimanin shekaru biyu kenan bayan nada shi Ministan sharia.

KU KARANTA; Zamu halaka duk wanda yayi mana katsalandan a zabe – El-Rufai ga yan kasashen waje

Allura ta tono garma: Atiku da Obasanjo na da hannu cikin kashe tsohon ministan sharia - Soyinka

Bola Ige
Source: UGC

A cewarsa, Obasanjo da Atiku suna da masaniya game da wanda ya kashe Soyinka ko kuma abinda ya kasheshi, kuma sun hana shari’a tayi aikinta akan koma wanene saboda wata bukatar kawunansu.

A cikin sanarwar mai taken ‘shashantar da rashawa, karya lagon adalci’, Soyinka ya koka kan tsagwarn cin hanci da rashawa daya mamaye Najeriyarmu a yau, inda yace; “Abin takaici ne ace wasu lauyoyi guda 20 sun dauki gabaran kare kazantar dake cikin fannin shari’a.”

Wannan batu na Soyinka baya rasa nasaba da bahallatsar tsohon Alkalin Alkalai, Walter Onnghen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallama, da yadda wasu lauyoyi suka yi kokarin kareshi duk kuwa da cewa an kama shi da laifin boye sama da naira biliyan 1.

“Har yanzu bamu dauki darasi daga bahallatsar kisan tsohon Ministan Sharia Bola Ige ba, wanda har yanzu ba’a warwareta ba, haka kungiyar lauyoyin Najeriya ta karbi uzurin tsohon shugabanta da tunanin magana ya kare, amma basu san mu kuwa a wajenmu tana nan danye ba.

“Gwamnati mai mulki a wancan zamani ta san wanda suka kashe Ige, amma ta karesu, sa’annan ta saka musu da gwaggwabar sakayya, inda shi kanwa uwar gamin ya samu sakayya da kujera a majalisar wakilai, har ma da karin shugabancin kwamitin kasafin kudinta.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel