Gwamna Ya Fadi Abin da Zai Yi Wa Tinubu idan Ya Zama Shugaban Kasa a Zaben 2027

Gwamna Ya Fadi Abin da Zai Yi Wa Tinubu idan Ya Zama Shugaban Kasa a Zaben 2027

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, Seyi Makinde, ya ce ba zai jawo Shugaba Bola Tinubu cikin gwamnatinsa ta haɗin kan ƙasa ba
  • Makinde ya zargi Tinubu da rashin cika yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa da suka cimma gabanin zaɓen 2023
  • Sai dai ya ce a shirye yake ya naɗa ƙwararrun ’yan APC waɗanda yake ganin za su iya taimakawa wajen tafiyar da gwamnati idan ya ci zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo, Nigeria - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya bayyana cewa ba zai jawo Shugaba Bola Tinubu cikin gwamnatinsa ta haɗin kan ƙasa ba idan ya samu nasarar lashe zaɓen 2027.

Makinde, gwamnan Jihar Oyo, ya zargi Tinubu da gaza cika yarjejeniyar da suka cimma gabanin babban zaɓen 2023, wadda ta shafi kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.

Kara karanta wannan

"Tikitina ya fi na Obi da Kwankwaso"; Dan takarar shugaban kasa ya kawo dalilinsa

Gwamna Makinde.
Gwamnan jihar Oyo kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Gwamna Makinde ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin The Rooftop Podcast.

Makinde ba zai yi aiki da Tinubu ba

Ya ce zai yi la’akari da naɗa ƙwararrun ’yan APC a gwamnatinsa, yana mai cewa akwai mutanen kirki a jam’iyya mai mulki waɗanda za su iya bayar da gudummawa wajen tafiyar da ƙasa.

A yayin hirar, an tambaye shi ko zai haɗa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, Peter Obi da Tinubu cikin gwamnatinsa idan ya zama shugaban ƙasa.

Amsar da ya bayar ita ce:

"Wataƙila ban da Shugaba Tinubu, amma har yanzu akwai mutanen kirki a cikin APC. Zan zaɓo wasu daga cikinsu, domin su ma ’yan Najeriya ne.”

Dalilin da ya sa ya ware Tinubu

Da aka tambaye shi ko hakan na nufin ba ya ganin Tinubu a matsayin mutumin kirki, gwamnan ya ce hakan ya samo asali ne daga irin gogewar da ya samu wajen aiki tare da shugaban ƙasar a lokacin zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake dawo da alkawarin da ya dauka a baya, ya roki yan Najeriya

Ya bayyana cewa sun cimma yarjejeniya kan kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, amma Tinubu bai cika abin da suka amince da shi ba.

Makinde ya ce:

"To, ba a wannan yanayin ba. Ina nufin na yi masa aiki a shekarar 2023. Mun amince da kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, amma bai cika yarjejeniyar ba.”

Gwamnan ya yi ƙarin bayani cewa batun gwamnatin haɗin kan ƙasa na daga cikin matsayar gwamnonin PDP G5, waɗanda suka raba gari da shugabannin jam’iyyarsu gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Gwamna Makinde.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Seyi Makinde, Bayo Onanuga
Source: Facebook

A cewarsa, gwamnonin sun nemi a kafa gwamnati wadda za ta haɗa ƙwararrun ’yan Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da suke ciki ba.

Ya ce burinsu shi ne a samar da gwamnati da za ta yi amfani da ƙwarewar mutane daga ko’ina cikin ƙasar domin magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Abubuwan da za su ba Makinde nasara

Kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde , ya ce ayyukan da ya gudanar a jihar Oyo na kimanin shekaru takwas sun ba shi kwarin gwiwar fuskantar babban zaɓen 2027.

Dan takarar APM ya ce ƙarin mafi ƙarancin albashi da biyan ma’aikata albashi a kan lokaci na daga cikin nasarorin gwamnatinsa a Oyo da za su iay ba shi nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262