YOFA: Kungiyar Matasan da ke yakin neman zaben PDP a Jihar Kano tayi sabon shugaba

YOFA: Kungiyar Matasan da ke yakin neman zaben PDP a Jihar Kano tayi sabon shugaba

Mun samu labari a makon nan cewa Kungiyar nan ta YOFA watau Youth for Atiku na bangaren jihar Kano ta nada wani sabon shugaba na rikon kwarya bayan murabus din tsohon shugaban ta.

YOFA: Kungiyar Matasan da ke yakin neman zaben PDP a Jihar Kano tayi sabon shugaba

Sabon shugaban Kungiyar YOFA da aka nada jiya (Hoto daga Nobel Hassan)
Source: Twitter

Ambasada Abbas Abdulrasheed wanda shi ne shugaban wannan kungiya ta Matasan jihar Kano da ke kokarin ganin jam’iyyar PDP tayi nasara a zaben 2019 ya ajiye mukamin na sa ne a Ranar Talata, 8 ga watan Junairun 2019.

Abdulrasheed ya bayyana wannan mataki da ya dauka ne a shafin sa na sada zumunta na Tuwita. Matashin yace ya ajiye mukamin ne saboda wasu dalilai da bai iya bayyana su ba inda yace yana mai yi wa kungiyar fatan alheri.

KU KATANTA: Siyasar Kano: Ganduje ya kaddamar da bincike kan Kwankwaso

Ba da dadewa bane dai kungiyar ta YOFA ta nada wani sabon shugaba na rikon kwarya bayan Ambasada Abbas bar matsayin na sa. Jiya ne Kungiyar ta Youth for Atiku ta sanar cewa ta zabi Abdulrahman Saminu domin ya maye gurbi.

Sai dai kuma daga baya mun samu labari cewa Abbas Abdlrasheed zai rike matsayin Darektan kudi a wannan tafiya bayan da ya ajiye kujerar shugaban kungiyar. Matasan dai sun sha alawashin ganin APC ta sha kashi a zaben bana.

Jiya kun ji cewa ‘Dan takarar PDP na shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sake tabbatarwa jama’a cewa idan ya samu mulkin Najeriya, zai samawa dinbin Matasa da Mata ayyukan yi idan ya samu mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel