Cikin Hotuna: Atiku ya gudanar da taron yakin neman zabe a jihar Zamfara
A yau Litinin 4 ga watan Fabrairu, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya girgiza magoya bayan sa yayin taron yakin neman zabe da ya gudanar cikin birnin Gusau na jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Yayin ci gaba da yawon shawagi da karade jihohi 36 domin neman goyon bayan al'umma sakamakon kusantowar babban zaben kasa, a yau Litinin, Atiku ya girgiza magoya bayan sa a jihar Zamfara.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon gwamna kuma wakilin shiyyar Kano ta Tsakiya a majlisar dattawa, Sanata Rabi'u Musa Kwankaso, ya halarci taron yakin neman zaben Atiku da aka gudanar da misalin karfe 10.00 na safiyar yau cikin birnin Gusau.
Cikin jawaban sa da ya zayyana, Atiku ya sha alwashin inganta harkokin tsaro a jihar Zamfara tare da habaka harkokin kasuwanci a yayin da ya cimma nasara ta kasancewa jagoran al'ummar Najeriya baki daya.
KARANTA KUMA: Tsaro: El Rufa'i zai yiwa sarakunan gargajiya ihsani a jihar Kaduna
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, furucin tsohon mataimakin shugaban kasar na inganta harkokin ya sosawa al'ummar Zamfara wurin da ya ke masu ciwo sakamakon yadda suke ci gaba da fuskantar barazanar ta'addanci ba ga birni ko kauyukan su ba.
Kazalika jaridar ta ruwaito cewa, Wazirin ya gudanar da taron yakin neman zaben sa a jiya Lahadi cikin Birnin Kebbi inda ya girgiza magoya baya na al'umma da suka cika kuma suka batse domin nuna tsagwaran soyayyar su.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng