Abin da Nafiu Bala Ya Fada wa Ƴan 'Takarar' ADC bayan Tara Su a Kaduna
- Shugaban ADC, Nafiu Bala Gombe, ya jagoranci ganawa da ‘yan takarar jam’iyyar domin daidaita shirye-shiryen yakin neman zabe gabanin babban zaben 2027
- Nafiu Bala Gombe ya bukaci yan tsagin ADC su koma mazabarsa domin yin cikakken rijistar zama yan jam’iyyar ADC kafin ya zama cikakken mamba
- Shugaban ADC ya bayyana cewa ya shirya nada Atiku Abubakar a cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Nafiu Bala Gombe, ta yi gudanar da taro a Kaduna.
ADC ta gudanar da wata ganawa ta musamman da ‘yan takararta domin tsara dabarun yakin neman zabe gabanin babban zaben shekarar 2027.

Source: Facebook
An gudanar da taron ne a cibiyar taron NCI International Conference Center da ke Kaduna, inda shugaban jam’iyyar na kasa, Hon. Nafiu Bala Gombe, ya jagoranci zaman, cewar The Guardian.
Manyan mutane da suka taron Nafiu Bala
Taron ya samu halartar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Farfesa Chris Uba, da mataimakinsa, Dakta Shamsuddeen Modibbo Barkindo, tare da ‘yan takarar gwamna da na majalisar dokoki ta kasa daga sassa daban-daban na Najeriya.
A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na jam’iyyar, Dakta Christopher Okechukwu, ya fitar, ya ce ganawar ta mayar da hankali ne wajen karfafa hadin kai, da’a da kuma daidaita ayyukan ‘yan takara da shugabannin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa manufar hakan ita ce gina yakin neman zabe na kasa baki daya da zai taimaka wa jam’iyyar wajen samun nasara a matakai daban-daban na zaben 2027.
A yayin jawabin nasa, Nafiu Bala Gombe ya ba tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar shawarari da za su kawo wa jam'iyyar nasara.
Nafiu Bala ya bukaci Atiku ya tabbatar da cewa ya sabunta katinsa na zama cikakken dan jam'iyyar.
Ya ce yin rijistar zai ba Atiku cikakken damar cin gajiyar hakkoki da sauran alfarmar da kundin tsarin jam’iyyar ya tanadar wa mambobinta.

Source: Twitter
Shirin Nafiu Bala ga Atiku Abubakar
Gombe ya kuma bayyana cewa zai yi la’akari da nada Atiku Abubakar a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na ADC a babban zaben 2027 bayan ya kammala rijistarsa.
Shugaban jam’iyyar ya ce kwarewar Atiku a siyasa, alakarsa da sassa daban-daban na Najeriya da fahimtarsa kan harkokin mulki za su taimaka wa ADC wajen kokarinta na kalubalantar gwamnatin APC da samar wa ‘yan Najeriya wani zabin siyasa.
Ya sake jaddada kudurin jam’iyyar na tabbatar da hadin kai, shugabanci mai bai wa kowa dama da kuma yakin neman zabe da zai dogara da muradun al’umma, cewar Punch.
Haka kuma, ya bukaci dukkan ‘yan takarar jam’iyyar da su koma mazabunsu domin wayar da kan jama’a, karfafa goyon bayan kasa-kasa da kuma hada kai da shugabannin ADC a dukkan matakai.
Rokon Nafiu Bala ga hukumar INEC
An ji cewa Nafiu Bala Gombe ya rubuta wa hukumar INEC wasika, yana sanar da ita cewa ya koma kan mukaminsa na shugaban jam’iyyar ADC na kasa.
Ya bukaci hukumar ta amince da shi a matsayin shugaban jam’iyyar tare da sabunta bayanan ADC da ke shafinta na intanet.
Wannan na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar karkashin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.
Asali: Legit.ng


