Cibiyar BBYDI Ta Biyo ta wajen Malamai da Sarakuna a Inganta Ilmin Mata a Kaduna
- Brain Builders Youth Development Initiative ta shiga wasu kananan hukumomin Kaduna domin bunkasa ilmi
- Cibiyar ta dage wajen ganin yara mata sun je makaranta, ba a bar su a baya ba wajen samun ilmi na zamani
- BBYDI ta biyo ta wajen malaman addini da sarakunan gargajiya a kokarin ganin babu abin da ya hana mata karatu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Shugabanni addini da sarakunan gargajiya sun shirya aiki da Brain Builders Youth Development Initiative (BBYDI) a jihar Kaduna.
Shugabannin za su hada-kai da cibiyar BBYDI domin ganin yara mata sun samu damar cigaba da karatu ba tare da sun ci karo da wasu matsaloli ba.

Source: Original
Kaduna: Cibiyar BBDYI ta shiga garuruwan Kaduna
Cibiyar ta sanar da haka a wani jawabi da ta fitar wanda ya shiga hannun Legit Hausa a makon jiya.

Kara karanta wannan
INEC ta fito ta bayyana dalilin da ya sa ba ta cire sunan Atiku daga jerin 'yan takara ba
BBYDI ta kuduri aniyar ganin ta taimaki yara matan da karatunsa ya tsaya a dalilin aure, juna biyu ko matsin tattalin arzikin da ya hana su shiga aji.
Sarakuna da jagororin addinin sun bayyana goyon bayansu ne a wajen taron rantsar da shugabannin gamayyar tafiyar ilmin ‘ya ‘ya mata da aka yi.
An rantsar da shugabannin gamayyar ne wani taro da aka shirya a otel din Asa Pyramid da ke garin Kaduna da taimakon gidauniyar nan ta Malala Fund.
BBYDI ta kuma kaddamar da kayan aikin wayar da kai mai dauke da harsunan gida da shugabannin za su yi amfani da shi don ilmin yara mata.
Cibiyar ta kuma yi amfani da wannan dama wajen fito da wasu dokoki da ka’idojin aikinsu.
BBYDI ta dage kan karatun yara mata
Gamayyar za ta dage wajen yakar kalubalen talauci, rashin tsaro, auren wuri da kuma matsin da yaran da suka yi ciki suke fuskanta a makaranta.
Darektar harkokin BBYDI, Halimat Olufade ta ce suna tattaunawa da malamai da shugabannin gargaji a kananan hukumomi 12 da suke aiki a Kaduna.
Olufade ta ce CAN da Jama’atu Nasril Islam (JNI) yi alkawarin yin amfani da masallatai da cocinsu domin su karfafi ilmin ‘ya ‘ya mata a cewar The Sun.
Musulmai da kiristocin za su maida hankali wajen ganin matan aure da iyayen yara sun cigaba da karatu.
Gwamnan Kaduna ya jinjina wa aikin BBYDI
Gwamna wato Malam Uba Sani ya yaba wa wannan kokari da BBYDI ta ke yi a jihar Kaduna.
Mai girma Uba Sani ya yi magana ne ta bakin Mallam Abass Shehu wanda ya wakilce shi, inda kuma ya yi bayanin kokarind a gwamnatinsa ta ke yi.
A karkashin shirin AGILE, gwamnatin jihar ta ce ta gina kuma ta gyara makarantu sannan ta tur awa yara mata 46, 572 kudi domin su ji dadin karatu.
Shi ma Kwamshinan ilmi, Farfesa Abubakar Sani Sambo ya jinjina, tare da bayanin kokarin yadda ma’aikatarsa za ta taka rawar gani a wannan bangare.
Tarihin karatun mata a masarautar Zazzau
Mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, ya ce kofar masarautarsa a bude ta ke a game da abin da ya shafi samar damar karatun ‘ya ‘ya mata.
Makaman Malamai, Sani Yusuf Magaji da ya wakilci sarki ya nuna yadda masarautar Zazzau ta ba karatun mata muhimmanci tun zamanin Jafaru dan Isyaku.
Sarki Jafaru Dan Isyaku, ya sa diyarsa Hajiya Talle a makarantar kwana ta mata ta Babban Dodo a lokacin da ya yi mulki tsakanin shekarar 1937 da 1959.
Sauran wadanda suka yi magana wajen taron sun hada da Rahanatu Lawal daga jami’ar ABU Zariya.

Source: Original
Mata sun samu horon amfani da AI daga BBYDI
A baya an ji labari BBYDI ta kaddamar da shirin 'SheBuilds AI Fellowship' na tsawon watanni shida a jihar Kaduna domin horar da mata 20 a fannin fasahar AI.
Gwamnatin Kanada ce ta dauki nauyin wannan shiri ta hanyar asusun CFLI domin rage gibin ilimin fasaha tsakanin maza da mata da kuma taimakon Arewa.
Shugaban cibiyar, Olasupo Abideen Opeyemi, ya yi kira ga gwamnati da ta saka irin wannan horo na AI, kimiyyar bayanai, da kasuwancin zamani cikin 3MTT
Asali: Legit.ng

