Hadarin jirgi: Na ji dadi da Osinbajo ya fita lafiya – Inji Atiku Abubakar

Hadarin jirgi: Na ji dadi da Osinbajo ya fita lafiya – Inji Atiku Abubakar

Mun ji labari cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi magana jiya bayan ya samu labari cewa jirgin Farfesa Yemi Osinbajo ya fadi a Garin Kabba da ke cikin jihar Kogi a jiya Asabar.

Hadarin jirgi: Na ji dadi da Osinbajo ya fita lafiya – Inji Atiku Abubakar
Atiku yayi murna bayan su Osinbajo su tsira a hadarin jirgi
Asali: UGC

Atiku Abubakar wanda yake neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta PDP ya ajiye sabanin siyasar da su ke da ita da Farfesa Yemi Osinbajo, bayan ya ji cewa mataimakin shugaban kasar ya gamu da hadarin jirgin sama jiya.

Mai girma Yemi Osinbajo ba bakon hadarin jirgin sama bane, inda ko a shekarar 2017, jirgin sa ya taba kifewa a Abuja. Jirgin saman da ke dauke da mataimakin shugaban kasar ya watse ne a cikin Garin Gwagwalada a wancan lokaci.

KU KARANTA: 2019: PDP ta gargadi INEC a game da yin magudi da APC

Mataimakin shugaban kasar ya tsira kalau wannan karo da jirgin yawon na shi ya fadi wajen sauka. Wannan ya sa aka ji Atiku Abubakar yana mai farin cikin jin cewa kowa ya tsira lafiya ba tare da samun wani rauni ko makamacin haka ba.

Alhaji Atiku Abubakar yayi maza ya aikawa mataimakin shugaban kasar wannan sako ne tun a jiya Asabar da rana ta shafin sa na sadarwa na Tuwita da kan sa, inda yayi murnar jin cewa mai girma Farfesa Osinbajo yana nan kalau.

Hakan na zuwa ne bayan da Alhaji Atiku Abubakar ya shiga jihar Abia yana yawon yakin neman zabe inda yayi kira ga jama’a su zabi jam’iyyar PDP a zaben bana domin Matasan kasar nan su samu aikin yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel