Matar Janar Aguyi-Ironsi za tayi wa Jam’iyyar PDP da Atiku aiki a zaben 2019

Matar Janar Aguyi-Ironsi za tayi wa Jam’iyyar PDP da Atiku aiki a zaben 2019

- Uwargidar Marigayi Johnson Aguiyi-Ironsi tayi magana game da zaben bana

- Madam Victoria Aguiyi-Ironsi za tayi kokarin ganin PDP tayi nasara a Abia

- Victoria ta kuma sha alwashin ganin Mata sun zabi Atiku Abubakar a zaben

Matar Janar Aguyi-Ironsi za tayi wa Jam’iyyar PDP da Atiku aiki a zaben 2019
Iyalin Aguyi-Ironsi za ta taya Atiku Abubakar yakin neman zabe
Asali: UGC

Mai dakin Marigayi tsohon shugaban kasa Janar JTU Aguiyi-Ironsi tsomo bakin ta game da zaben da za ayi shekarar nan. Inda ta fitar da zabi tsakanin Alhaji Atiku Abubakar na PDP da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari na APC.

Madam Victoria, wanda ita ce Marigayi Janar Johnson Aguiyi-Ironsi, ya bar Duniya ya bari, tayi alkawarin taya jam’iyyar PDP yakin neman zabe a bana. Victoria Aguiyi-Ironsi ta bayyanawa Matar gwamnan Abia wannan ne jiya.

KU KARANTA: 2019: Jikan Shehu Inyass yana neman kujerar Gwamna a Najeriya

Matar Marigayin ta tabbatar da cewa za ta dage wajen ganin Matan jihar Abia sun zabi PDP domin ganin an gyara kasar nan. Victoria Ironsi tace za tayi aiki da Nkechi Caroline Ikpeazu wanda ita ce Mai dakin mai girma gwamna Ikpeazu.

Kamar yadda mu ka ji, Uwargidar tsohon shugaban kasar a lokacin soji tayi wannan jawabi ne a wajen wani taro na musamman da aka shiryawa Matan PDP da ke jihar Abia a kudancin Najeriya a jiya Laraba 16 ga Watan Junairun 2019.

Victoria Aguiyi-Ironsi tace za ta jagoranci jama’a musamman ‘yan uwan ta mata su marawa PDP da Atiku baya a zaben da za ayi, Ironsi tayi wannan magana ne tana mai tabbacin cewa matan jihar ba za su yi da-na-sanin wannan zabi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng