Atiku Abubakar yayi alkawarin samawa Matasa da Mata aikin yi a Najeriya

Atiku Abubakar yayi alkawarin samawa Matasa da Mata aikin yi a Najeriya

‘Dan takarar PDP na shugaban kasa a zaben da za ayi kwanan nan, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake tabbatarwa jama’a cewa idan ya samu mulkin Najeriya, zai samawa dinbin jama’a ayyukan yi.

Atiku Abubakar yayi alkawarin samawa Matasa da Mata aikin yi a Najeriya

Atiku yace a zabi PDP tun da Gwamnatin Buhari ta sa mutane da dama sun rasa aikin yi
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya bayyana wannan ne lokacin da jam’iyyar PDP tayi taron kamfen din ta a Garin Minna a cikin jihar Neja. Atiku ya sha alwashin nemawa jama’a hanyar samun aikin da sana’o’i inda yace gwamnatin nan ta gaza.

Atiku yayi ikirarin cewa gwamnatin Buhari tayi sanadiyyar rasa aikin mutane fiye da miliyan 10 a cikin shekaru 3 da rabi da yayi yana kan mulki. A dalilin haka ne Atiku yayi kira ga jama’a su guji sake zaben APC a abban zaben bana.

KU KARANTA: Kalaman Bola Tinubu a kan Atiku Abubakar sun jawo masa matsala

Tsohon mataimakin shugaban kasar yayi kira a zabi PDP domin kuwa a cewar sa gwamnatin nan ta APC ta gaza cika alkawuran da ta dauka na yaki da cin hanci da kuma kawo karshen sha’anin tsaro tare da inganta tattalin kasa.

‘Dan takarar na PDP ya nuna cewa akwai bukatar a sake gina hanyoyi da makarantu da asibitoci a kasar inda ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin sa da saukaka harkar kasuwanci da neman kudi domin rage radadin talauci a kasar.

Sauran wadanda su ka halarci wannan babban taro sun hada da manyan ‘yan PDP irin su Bukola Saraki, Umaru Nasko, Tanimu Turaki, Rabiu Kwankwaso, Phillip Aduda, Shem Zagbayi da Sanata Zainab Kure.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel