Atiku Abubakar ya nemi Magu ya binciki tabargazar da ake yi a Hukumar BCDA

Atiku Abubakar ya nemi Magu ya binciki tabargazar da ake yi a Hukumar BCDA

- Atiku ya nemi Jami’an Gwamnati su binciki Surukin Shugaban kasa

- ‘Dan takaran na PDP yana zargin Shugaban Hukumar BCDA da laifi

- Yace BCDA na amfani da dukiyar Gwamnati wajen taya Buhari kamfe

Atiku Abubakar ya nemi Magu ya binciki tabargazar da ake yi a Hukumar BCDA
Atiku yana zargin hukumar Border Communities Development Agency da barna
Asali: Twitter

‘Dan takaran jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar yana neman hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da kuma hukumar ICPC mai yaki da barayin kasar nan ta tuhumi shugaban hukumar BCDA.

Atiku Abubakar yana zargin Kyaftin Junaid Abdullahi, wanda yake rike da hukumar BCDA mai kula da yankunan da ke kan iyakokin Najeriya, da amfani da hukumar gwamnati wajen yi wa shugaban kasa Buhari kamfe a zabe sa.

KU KARANTA: Yadda Surukin Buhari yake sabawa dokar aiki a Hukumar BDCA

Atiku wanda shi ne babban Abokin hamayyar Buhari yayi wannan jawabi ne ta wani Hadimin sa, Phrank Shuabu. ‘Dan takarar na PDP yana zargin Kyaftin Abdullahi da amfani da ofishin sa wajen yi wa jam’iyyar APC yakin neman zabe.

Phrank Shuabu yace BCDA ta bada wasu kwangiloli da su ka sabawa ka’idar aiki domin a sulale da kudin da za ayi wa APC yakin tazarce a zaben bana. Shugaban hukuma rna BCDA, Suruki ne wurin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

‘Dan takarar yace yaki da cin hanci da rashawa da ake yi ya zama wasa idan har aka kyale shugaban na hukumar BCDA yana abin da ya ga dama na bada kwangilolin miliyoyi na iska Don haka ya nemi jami’an EFCC da ICPC su yi aikin su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel