Atiku Abubakar
Atiku ya taki sa’a bayan sakamakon zaben Kaduna ya fara fitowa bayan dogon lokaci. Jam’iyyar PDP ta fara 2019 a Kaduna da Bismillah inda aka ji Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasara a karamar hukumar Kaura.
Mun ji cewa Atiku ya bayyana ainihin abin da ya sa ya shiga siyasa a Najeriya. Atiku yace abin da yake so shi ne ya ga wanda ba ‘Dan kowa ba ya zama kowa. Atiku yace wannan shi ne babban burin da yake ke da shi a siyasar Najeriya.
Fitaccen Sanatan nan Dino Melaye yace zai rabawa Mutane 10 Miliyan guda idan Atiku yayi nasara. Sanatan yace mutane 10 za su samu Miliyan 1 a hannun sa amma fa idan Atiku ya lashe zaben 2019 da za ayi a makon gobe.
Mun ji cewa Jam’iyyar APC tace manyan kasashen Duniya ba su tare da Buhari inda su ke ganin Amurka su na goyon bayan Atiku a ka zaben bana. Festus Keyamo yace Kasashen waje na nuna fifiko ne ga Jam’iyyar PDP.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe cikin tsohon birni na Kano Dabo yayin cika da batsewa ta dumbin magoya baya.
Mun samu cewa, masu sayar da jar Tagiya a yau Lahadi cikin birnin Kano sun dara wajen cin kasuwar su a harabar filin wasanni na Sani Abacha yayin taron yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da aka gudanar.
Ko shakka ba bu birnin Kano ya cika ya batse yayin da magoyo baya tamkar ridi suka yi turuwa sanye da jajeyen huluna domin yiwa Wazirin Adamawa kyakkyawar tarba da bai samu makamanciyar ta ba a duk ilahirin jihohin Najeriya.
Titi Abubakar, daya daga cikin Matan dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ta ce ba bu wata makawa Mijin ta zai zamto shugaban kasar Najeriya a yayin babban zabe da za a gudanar a ranar Asabar.
Ana daf da zabe ne aka ji an gano cewa Atiku Abubakar ba Mutumin Najeriya bane kamar yadda mu ka ji.A tsarin mulkin Najeriya, bai halatta mutum ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa ba, har sai idan ‘dan kasa ne.
Atiku Abubakar
Samu kari