Ana zargin cewa Atiku Abubakar ba haifaffen cikin Najeriya bane

Ana zargin cewa Atiku Abubakar ba haifaffen cikin Najeriya bane

Mun samu labari cewa wasu sun fara kira a dakatar da ‘dan takarar jam'iyyar PDP na shugaban kasa a zaben 2019 watau Alhaji Atiku Abubakar daga takara inda ake zargin cewa ba a Najeriya aka haife sa ba.

Ana zargin cewa Atiku Abubakar ba haifaffen cikin Najeriya bane
Wasu na ikirarin a wajen Najeriya aka haifi Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Dr. Bunmi Awoyemi yayi wani rubutu a cikin makon nan inda yake cewa Atiku Abubakar ba haifaffen ‘Dan Najeriya bane. Marubucin yace an haifi Atiku ne a wani karamin gari ne da ake kira Jada wanda a da yankin na cikin kasar Kamaru.

Sai bayan an haifi Atiku Abubakar da dadewa ne sannan yankin Jada da kewaye na Arewacin kasar Kamaru su ka shigo cikin Najeriya. Wannan ya sa wasu ke ganin cewa dokar kasar nan ta haramtawa Atiku tsayawa takara a Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnan Anambra yace Buhari zai kara wata Jiha a kasar Ibo

A tsarin mulki, bai halatta mutum ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa ba, har sai idan an haife sa a Najeriya. Kauyen da Atiku Abubakar ya fito kuwa bai zama cikin Najeriya ba sai kusan bayan yayi shekaru 15 da haihuwa a Duniya.

Haka zalika kuma dokar Najeriya na cewa kafin mutum ya zama haifaffen ‘dan Najeriya, dole ya zama cewa an haife sa ne a cikin kasar kafin samun ‘yancin kai. Najeriya ta samu ‘yancin kai daga mulkin mallaka ne a farkon Oktoban 1960.

Sai dai tuni kuma Masana irin su Abdul Mahmud wanda kwararren Lawya ne yayi kaca-kaca da wannan magana inda yace yankin na Adamawa da ma kasar Taraba ba su taba shiga cikin tsantsar kasar Kamaru a wancan lokaci ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel