Kotu ta hana Atiku amfani da kimiyyar zamani wajen binciken kayayyakin zabe

Kotu ta hana Atiku amfani da kimiyyar zamani wajen binciken kayayyakin zabe

A jiya Laraba, kotun sauraron korafe-korafen zabe reshen kotun daukaka kara ta Najeriya, ta umarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta bai wa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyar PDP, Atiku Abubakar, damar gudanar da bincike kan kayayyakin da ta ribata yayin gudanar da babban zaben kasa a watan da ya gabata.

Wannan umarni ya bayu biyo bayan hukuncin kotun mai kunshe da manyan alkalai uku, inda ta nemi hukumar INEC ta yi gaggawar mika wa Atiku kayayyakin da ta ribata wajen gudanar da babban zaben kasa cikin kowace rumfar zabe da ke fadin kasar nan.

Tsohon mataimakin shugaban kasa na ci gaba da tayar da balli tare da kalubalanta gami da bayyana rashin amincewa da sakamakon zaben kasa inda ya ke ikirarin miyagun ababe na murdiya da magudi sun auku yayin gudanar da zaben a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Kotu ta hana Atiku amfani da kimiyyar zamani wajen binciken kayayyakin zabe
Kotu ta hana Atiku amfani da kimiyyar zamani wajen binciken kayayyakin zabe
Asali: Twitter

Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar Atiku ta neman amfani da kimiyya da kuma fasahar zamani wato Forensic Investigation, wajen gudanar da bincike kan muhimman kayayyakin na zabe musamman takardun dangwala kuri'u da kuma na'urar tantance katin zabe ta Card Reader.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Atiku ya ribaci shimfidar doka ta bai wa duk wani mai kalubalantar sakamakon zabe kwanaki 21 domin shigar korafi gabanin bayyanar sakamakon zabe, inda a halin yanzu ya samu kunnen sauraro na kotun karbar korafe-korafen zabe ta Tribunal.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar Arewa a fadar sa ta Villa

Kotun cikin bayyana dalilan ta na haramtawa Atiku amfani da kimiyya da fasahar zamani wajen aiwatar da binciken kan kayayyakin zabe, ta ce bukatar sa na cin karo da shimfidar tanadin sashe na 151 cikin kundin tsarin hukumar zabe ta Najeriya.

Babban alkali da ya yi jagoranci wajen zartar da wannan hukunci, Mai Shari'a Abdul Aboki, ya ce sashe na 151 cikin kundin tsari na hukumar INEC ya haramta amfani da kimiyya ko kuma fasahar zamani ta kwararru wajen gudanar da bincike kan muhimman kayayyakin zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel