Sarkin Kano ya yi kira kan tabbatar da zaman lafiya yayin zaben 2019

Sarkin Kano ya yi kira kan tabbatar da zaman lafiya yayin zaben 2019

A ranar Lahadin da ta gabata ne dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe a tsohon birni na Kano Dabo cikin cika da batsewa ta dumbin magoya baya.

Mun samu cewa, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya gargadi al'ummar Najeriya da su kauracewa duk wasu miyagun ababe tare da shawartar su kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali yayin babban zaben kasa da za a gudanar tsakanin watan Fabrairu da Maris.

Mai Martaba Sarki Sanusi ya yi wannan babbar huduba ta shawara da kuma jan hankali yayin da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kai ziyarar ban girma har fadar sa a jiya Lahadi da ke tantangwaryar birnin Kano.

Fadar Mai Martaba Sarki Sanusi yayin ziyarar Atiku da tawagar sa

Fadar Mai Martaba Sarki Sanusi yayin ziyarar Atiku da tawagar sa
Source: Twitter

Cikin hudubar sa, kasancewar sa Uba ga al'umma, Sarki Sanusi ya ce, "zabe ba yaki bane saboda haka ba bu wani dalili na zubar da jinin al'umma kuma ba bu wata alkarya da za ta taka mataki na ci gaba matukar ba bu zaman lafiya a tsakanin ta".

Yayin ci gaba da kiran sa, Sarkin Kano ya kuma ja hankalin al'umma kan zaben shugabanni macancanta domin samun kyakkyawan riko na akalar jagorancin su ta hanyar fidda kasar nan zuwa tudun tsira.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito, Sarki Sanusi yayin kwarara addu'o'i na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan, ya kuma kirayi al'umma da su mallaki katin zabe da a cewar sa shine babban makami na kwatar 'yanci.

Da yake mika godiyar sa kan wannan ziyara tare da fatan kwashewa lafiya yayin taron yakin zabe, babban basaraken ya kuma yabawa Atiku dangane da gudunmuwar sa akan ci gaban ilimi bisa la'akari da Jami'ar da ya assasa a mahaifar sa ta jihar Adamawa.

Cikin nasa jawaban, Atiku ya ce neman tabarrakin Iyayen kasa ita ce babbar manufa ta kawo ziyara fadar Mai Martaba Sarki Sanusi, inda ya misalta Sarakunan gargajiya a matsayin tubali da kuma ginshiki na tabbatar da hadin kai.

KARANTA KUMA: Yakin Zabe: An ci kasuwar jar hula a jihar Kano

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tawagar Atiku da ta ziyarci fadar Mai Martaba Sarki Sanusi ta hadar da shugaban jam'iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus, shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso.

Sauran 'yan tawagar sun hadar da tsohon Ministan harkokin kasashen waje, Alhaji Aminu Wali, tsohon Ministan Makamashi, Alhaji Tanimu Turaki, Sanata Abdul Ningi, Hajiya Baraka Umar, abokin takarar Atiku, Peter Obi da kuma dan takarar gwamnan Kano na PDP, Abba Kabir Yusuf.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel