Jigo a ADC Ya Fito da Wanda Atiku Zai Iya Janye Wa Takara a Zaben 2027
- Mawallafin mujallar Ovation International, Dele Momodu, ya ce Atiku Abubakar na nan cikin masu neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027
- Momodu ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba shi da niyyar janyewa domin barin wani ɗan takara, kuma yana da burin fafatawa
- Ya ce Atiku na da shirin inganta rayuwar ’yan Najeriya ta hanyar rage tsadar rayuwa, ƙarƙashin manufar samar da rayuwa mai sauƙi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shahararren ɗan jarida, ɗan kasuwa a harkokin yaɗa labarai kuma mawallafin mujallar Ovation International, Dele Momodu, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar na nan cikin takarar shugaban ƙasa ta 2027.
Momodu ya bayyana cewa Atiku ba shi da wani shirin janyewa domin barin wani ɗan takara, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuduri aniyar fafatawa a zaɓen.

Source: Twitter
Abin da Momodu ya ce kan Atiku
Jigon na jam'iyyar ADC ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, 22 ga Nuwamba, 2026.
A cikin saƙon, Momodu ya dage cewa Atiku ya shirya tsaf domin shiga zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, kuma babu wani ɗan takara da zai sa ya janye.
Ya rubuta cewa:
“Ku ɗauki wannan daga gare ni a matsayin cikakkiyar gaskiya… Atiku Abubakar mutum ne mai muhimmanci a siyasa, gogagge kuma mai mayar da hankali, don haka ba zai janye wa kowa ba.”
Atiku na son rage tsadar rayuwa, in ji Momodu
Mawallafin mujallar Ovation International ya ƙara da cewa Atiku na nan daram a cikin takarar, kuma yana da burin dawo da sauƙin rayuwa ga ’yan Najeriya.
A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban ƙasar na da niyyar ganin an samar da yanayin rayuwa mai sauƙi, musamman ta fuskar tsadar kayayyaki da sauran matsalolin da jama'a ke fuskanta.

Kara karanta wannan
Jonathan ya fito da sabuwar magana kan dalilinsa na mika mulki ga Buhari cikin sauki
Momodu ya ce:
"Yana nan sosai cikin takarar, kuma a shirye yake ya sake samar da rayuwa mai sauƙi ga dukkan ’yan Najeriya.”
Sanarwar Momodu ta zo ne a daidai lokacin da ake yaɗa saƙonni daban-daban kan matsayin Atiku a takarar shugaban ƙasa ta 2027.
Atiku Abubakar dai ya sha bayar da tabbacin cewa zai yi takara a zaben shugaban kasa na 2027 kuma ba zai janyewa kowa ba.

Source: Twitter
Kotu ta yi watsi da bukatar Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar Atiku Abubakar, na gabatar da sababbin hujjoji a ƙarar da ya shigar domin neman hana Shugaba Bola Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.
Alƙalin kotun ya amince da hujjojin lauyoyin Tinubu, APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), waɗanda suka nuna cewa amincewa da sababbin hujjojin zai sauya yanayin ƙarar tun farko.
Hakazalika, alƙalin ya kuma yi watsi da hujjar Atiku cewa gyaran da yake nema ba zai ƙara wasu sababbin batutuwa cikin ƙarar ba.
Asali: Legit.ng
