EFCC: Wani ‘Dan Atiku Abubakar ya caccaki Gwamnatin Buhari

EFCC: Wani ‘Dan Atiku Abubakar ya caccaki Gwamnatin Buhari

Mun samu labari cewa Mustapha Atiku Abubakar, wanda babban ‘dan cikin Atiku Abubakar ne, yayi tir da gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsare ‘yanuwan sa.

EFCC: Wani ‘Dan Atiku Abubakar ya caccaki Gwamnatin Buhari
Hukumar EFCC ta kama Lauya da wani Surukin Atiku
Asali: Twitter

Mustapha Abubakar, yayi wannan jawabi ne ta shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita bayan da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama wani babban Lauyan Atiku da wani Surukin sa.

Mustapha Abubakar, yace damke Surukin Mahaifin na sa da aka yi, ba komai bane illa kokarin ganin an hana babban Abokin hamayyar na shugaba Buhari magana, a dalilin shirin da yake yi na zuwa gaban kotu game da zaben 2019.

KU KARANTA: EFCC ta karbe wasu kudi daga aka sacewa Gwamnati kwanaki

Alhaji Mustapha Abubakar yace duk inda aka je aka dawo, ba a canzawa tuwo suna, kuma mutum bai taba canzawa, inda ce har yanzu shugaba Buhari yanan nan a yadda aka san sa na mai keta alfarmar mutane da danne hakkin su.

Yaron ‘dan takarar shugaban kasar na PDP yace ko sau nawa Buhari yayi takara a farar hula, ba zai sa ya tashi daga wanda ya saba kama-karya a gidan soja ba. Atiku yace duk wannan yunkuri da gwamnati ke yi ba zai kai ko ina ba.

Yanzu haka ma dai wani babban Lauyan Atiku mai suna Uyi Osagie yana hannun EFCC. Buhari dai ya lallasa Atiku ne a zaben shugaban kasa da aka yi kwanan nan inda tsohon mataimakin shugaban kasar ya kudiri niyyar zuwa kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel