Matawalle Ya Raba Motoci 1000 za Su Shiga Lunguna Nemawa Tinubu Kuri'u
- Ƙungiyar Tinubu Again Movement mai samun goyon bayan ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ta ce tana shirin samar da ƙuri’a miliyan 20
- Ƙungiyar ta kuma bayyana shirin rabon tallafin fara sana’a ga mutum 20,000, tare da raba motoci da babura 1,000 ga magoya bayan ta
- Rahotanni sun nuna cewa shugabannin kungiyar ta ce shirye-shiryen tallafin da take yi za su amfani mutane 100,000 a faɗin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ƙungiyar siyasa mai suna Tinubu Again Movement, wadda ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ke marawa baya, ta bayyana shirinta na taimakawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da ita a Abuja, inda ta ce ta tsara hanyoyin da za ta bi wajen wayar da kan magoya baya da kuma tara ƙuri’u a faɗin ƙasar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Matawalle ya nuna kwarin gwiwar cewa ƙungiyar za ta cimma burinta na samar wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20.
Shirin tallafa wa mutum 100,000
Matawalle ya bayyana cewa ƙungiyar za ta gudanar da shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arzikin al’umma, ciki har da tallafin fara sana’a ga mutum 20,000.
Ya ce za a kuma raba motoci da babura 1,000, tare da wasu nau’o’in tallafi da ake sa ran za su amfani mutane 100,000.
A cewar karamin ministan tsaron, an kafa ƙungiyar ne domin tallata manufofin Shugaba Tinubu na Renewed Hope Agenda.
Ya yi ikirarin cewa manufofin sun taimaka wajen bunƙasa abubuwan more rayuwa, sufuri, noma, ilimi, samar da iskar gas da kuma ƙarfafa tattalin arzikin al’umma.
Bello Matawalle zai tara kuri'a miliyan 20
Ministan ya ce ƙungiyar ta tanadi dabarun da za ta yi amfani da su wajen tattara magoya baya a dukkan sassan Najeriya domin tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027
Ya jaddada cewa mambobinta sun shirya tsaf domin cika alƙawarin da suka ɗauka na samar da ƙuri’u miliyan 20 ga shugaban ƙasar.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya nuna shakku kan jajircewar wasu ’yan takarar jam’iyyun adawa.
Ya yi tambaya kan dalilin da ya sa ’ya’yan wasu ’yan takarar ba sa fitowa wajen harkokin siyasa, yana mai cewa hakan na iya nuna rashin amincewarsu da shugabancin iyayensu.

Source: Twitter
Bello Matawalle ya kasance mai kula da harkokin APC a shiyyar Arewa maso Yamma a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023.
Tinubu ya samu matsala a Aso Villa
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce ’yan Najeriya ba su san irin ƙalubalen da yake fuskanta a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake ba da labarin yadda ruwa ya ɗauke masa yayin da yake aske gemunsa a ranar Laraba ta makon da ya gabata.
Shugaban kasar ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi, yayin wani taron addu’a na musamman da iyalansa suka shirya masa a jihar Legas.
Asali: Legit.ng
