Zargin Cin Zarafi: Sarkin Daura Ya Shiga Matsala bayan Yaɗuwar Bidiyonsa a Intanet
- Amnesty ta nuna damuwa kan zargin cin zarafin wata mata da ake yi wa Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk
- Wata mata ’yar yawon bude ido daga ketare ta zargi Sarkin Daura da taba jikinta ba tare da izininta ba lokacin da ta kai masa ziyara
- Kungiyar kare hakkin bil’adama ta bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Daura, Katsina - Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International reshen Najeriya ta bukaci gwamnatin jihar Katsina da rundunar ’yan sanda su binciki Sarkin Daura.
Hakan ya biyo bayan zargin cin zarafin wata mata yar yawon bude ido da aka alakanta da Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, kungiyar ta bayyana zargin a matsayin abin damuwa, tare da kira ga hukumomi da su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa.
Zargin Sarkin Daura da matar ke yi
Wata mata ’yar asalin wata kasa da ta ziyarci fadar sarkin ta yi zargin cewa ya taba jikinta ta hanyar da ba ta dace ba ba tare da izininta ba.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 14 ga watan Nuwamban 2026, lokacin da matar ke ziyartar fadar Sarkin Daura da ke jihar Katsina.
Amnesty International ta ce wasu bidiyoyi da matar ta wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna abin da ta bayyana a matsayin kokarin cin zarafinta ta hanyar lalata, duk da cewa tana nuna rashin amincewa.
Kungiyar ta kara da cewa matar ta yi zargin sarkin ya rika taba jikinta ta hanyoyin da ba ta amince da su ba a lokuta daban-daban.

Source: Original
Sarkin Daura: Amnesty ta yi Allah-wadai
Ta yi Allah wadai da irin wannan zargi, inda ta bukaci a tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da laifi bayan kammala bincike da bin tsarin shari'a.
A cikin sanarwar, Amnesty ta ce:
“Gwamnatin jihar Katsina da rundunar ’yan sandan Najeriya dole ne su gaggauta gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya domin tabbatar da cewa sarkin ya amsa tambayoyi kan zargin yunkurin cin zarafinta.”
Sai dai kungiyar ta jaddada cewa duk wani mataki na gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu dole ne ya bi ka'idojin shari'a, tare da tabbatar da an ba shi damar kare kansa cikin adalci.
Haka kuma, ta bayyana cewa bai kamata a sanya hukuncin kisa cikin irin hukuncin da za a yanke kan wannan zargi ba.
Kungiyar ta ce wannan lamari wata dama ce ga hukumomin Najeriya su nuna cewa babu wani mutum da ya fi karfin doka, komai matsayinsa a cikin al'umma.
Ta kuma danganta lamarin da yadda ake nuna wa cin zarafin mata kamar abubuwan da suka zama ruwan dare, tana mai gargadin cewa masu aikata irin wadannan laifuka kan tsallake hukunci.
Tun da farko, matar ta wallafa bayaninta a kafafen sada zumunta, inda ta zargi sarkin da taba nonuwanta ba tare da izininta ba. Ta ce ta nuna rashin amincewarta a lokacin da abin ya faru.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, majalisar masarautar Daura da wakilan sarkin ba su fitar da wata sanarwa kan zargin ba.
Amnesty ta bukaci cafke ciyaman a Kano
Mun ba ku labarin cewa kungiyar Amnesty ta soki shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Abubakar Ma’azu Mojo, bisa wasu kalamansa.
An zargi shugaban ƙaramar hukumar da ƙarfafa amfani da barazana, tashin hankali da daba domin karɓe rumfunan zaɓe daga yan adawa.
Amnesty ta buƙaci hukumomin tsaro su ɗauki mataki, tana gargadin cewa irin waɗannan kalamai na iya tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a.
Asali: Legit.ng


