Tarihin babban Lauyan Atiku Abubakar Dr. Livy Uzoukwu SAN

Tarihin babban Lauyan Atiku Abubakar Dr. Livy Uzoukwu SAN

Yayin da ake ta fama da shirin shari’a a game da zaben 2019 inda ‘dan takarar PDP Atiku Abubakar yake kalubalantar sakamakon zaben na bana mun kawo jerin kwararrun Lauyoyin da ake ji da su, da ‘dan takarar ya dauko haya.

Babban Lauyan Atiku a kotun sauraron karar zaben shi ne Dr. Livy Uzoukwu (SAN). Sauran manyan Lauyoyin da ke cikin tawagar Atiku Abubakar sun hada da Kabiru Tanimu Turaki, Chris Uche, Emeka Etiba, da Mike Ozekhome.

Wadannan Lauyoyi da ke kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari ba su tsaya a nan ba, inda su ka hada da kuma manyan Lauyoyi irin su Eyitayo Jegede, Maxwell Gidado da sauran Lauyoyi akalla 10 da ba a ambata a nan ba.

KU KARANTA: Zaben 2019 ya sa ana neman tonawa Shugaba Buhari da Atiku asiri

Dr. Livy Uzoukwu wanda shi ne shugaban wannan gayya ba sabon-shiga harkar shari’a bane domin kuwa yayi Digirinsa a fannin tun 1981, inda ya tsunduma cikin wannan aiki a 1982, sannan kuma ya koma yayi Digiri na biyu a 1991.

Livy Uzoukwu ya samu shaidar zama Dakta a harkar shari’a bayan yayi Digirin san a PhD a wata jami’a a kasar Afrika ta Kudu a 2010. Tun a 1994, Uzoukwu ya kafa tarihi inda ya rike Kwamishinan shari’a a jihar Imo a sa'ilin yana Matashi.

KU KARANTA: Uwargidar Shugaban kasa ta na da sha'awar bude Jami'ar Buhari

Bayan wannan mukami iri-iri da ya rike a jihar Imo, Uzoukwu, yana cikin kwamitin manyan Lauyoyin da ake ji da su tun tsakanin 1994 zuwa 1996, inda ya kasance cikin masu ba gwamnatin Najeriya shawarwari a kan harkokin shari’a.

A shekarar 2008 ne, gwamnatin tarayya ta karrama wannan babbam Lauya da sandar girma ta Order of Niger (watau OON) saboda kwazon sa. Yanzu haka Dr. LIVY UZOUKWU LL.B, LL.M, LLD, SAN, OON shi ne babban wanda ya tsayawa Atiku a kotu.

Abin da jama’a da dama ba su sani ba shi ne har da Abokin takarar Atiku a zaben fitar da gwani na PDP cikin Lauyoyinsa a Kotu. Wannan ba kowa bane illa tsohon Ministan PDP Kabiru Tanimu Turaki SAN.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel