Sanata Dino Melaye zai rabawa Mutane 10 Miliyan guda idan Atiku yayi nasara

Sanata Dino Melaye zai rabawa Mutane 10 Miliyan guda idan Atiku yayi nasara

- Dino Melaye zai raba Miliyan 10 idan APC ta sha kasa a zaben bana

- Sanatan na PDP yace zai zabi Mutane 10 ne da zai rabawa Miliyan 1

- Melaye ya shiga sarkakiya iri-iri da jami’an tsaro 'yan kwanakin nan

Sanata Dino Melaye zai rabawa Mutane 10 Miliyan guda idan Atiku yayi nasara

Mutane za su samu kyauta daga Sanata Melaye idan Atiku ya ci zabe
Source: Twitter

Mun samu labari kwanan nan cewa Sanatan nan na yankin jihar Kogi ta yamma watau Mista Dino Melaye, ya bayyana cewa zai raba makudan kudi, muddin jam’iyyar hamayya PDP ta samu nasara a zaben da za ayi mako mai zuwa.

Dino Melaye wanda yayi fice a Najeriya, yayi alkawarin cewa zai zabi wasu mutum 10 da zai rabawa kudi har Naira miliyan 10, idan aka yi dace jam’iyyar sa mai adawa ta PDP ta kai labari a zaben shugaban kasa a makon gobe.

KU KARANTA: Mai neman Sanata a APC ne ya yi kwangilar kayan aikin zabe – inji INEC

Fitaccen Sanatan ya bayyana wannan ne a shafin sa na Tuwita a Ranar Asabar 16 ga Watan nan. Sanatan ya bayyana wannan ne a ranar da aka sanar da cewa INEC ta dakatar da zaben shugaban kasa zai wani mako mai zuwa.

‘Dan majalisar na yammacin Jihar Kogi yake cewa zai zabi wadanda zai ba wannan kudi har Naira miliyan guda ne daga cikin masu bibiyar sa a kafafen sadarwa. Don haka ne Sanatan yayi kira ga jama’a su yada wannan sako.

Kwanan nan ne Sanatan ya bayyana cewa wasu sun yi yunkurin sace sa a lokacin da yake tafiya a hanyar Lokoja. ‘Dan majalisar dai ya ba wani mutumi kyautar N2000 kwanan nan bayan yayi tattaki domin ya hadu da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel