Kamfe: Atiku ya gigita al'ummar jihar Kano

Kamfe: Atiku ya gigita al'ummar jihar Kano

Mun samu cewa a yau Lahadi, 10 ga watan Fabrairu, 2019, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gudanar da yakin neman zaben sa cikin salo a jihar Kano ta Dabo Tumbin Giwa.

Ko shakka ba bu birnin Kano ya cika ya batse yayin da magoyo baya tamkar ridi suka yi turuwa sanye da jajeyen huluna domin yiwa Wazirin Adamawa kyakkyawar tarba da bai samu makamanciyar ta ba a duk ilahirin jihohin Najeriya.

Bayan dirar Atiku a safiyar yau ta Lahadi tare da jiga-jigan jam'iyyar PDP na kasa da suka hadar da shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da kuma shugaban jam'iyyar na kasa, Prince Uche Secondus, sun kuma kama hanyar su ta kai ziyarar ban girma fadar Mai Martaba San Kano, Muhammadu Sanusi II.

Alkaluman siyasa sun tabbatar da cewa, Atiku ya samu goyon bayan al'ummar jihar Kano a sakamakon rawar da tsohon gwamnan jihar ya taka, Sanata Rabi'u Kwankwaso, da aka yiwa lakabi da madugu uban tafiya.

Atiku yayin isowar sa jihar Kano

Atiku yayin isowar sa jihar Kano
Source: Twitter

Bukola Saraki yayin saukar sa tare da Atiku a jihar Kano

Bukola Saraki yayin saukar sa tare da Atiku a jihar Kano
Source: Twitter

KARANTA KUMA: APC-ta-shiga-rudu: Shugaba Buhari ya kasa daga hannun dan takara a jihar Zamfara

Madugu Kwankwaso yayin tarbar Atiku da tawagar sa a filin jirgin sa na Mallam Aminu Kano

Madugu Kwankwaso yayin tarbar Atiku da tawagar sa a filin jirgin sa na Mallam Aminu Kano
Source: Twitter

Tawagar Atiku akan hanyar kai ziyarar ban girma fadar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Tawagar Atiku yayin da ta ke daf da fadar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Tawagar Atiku yayin da ta ke daf da fadar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Source: Twitter

Tawagar Atiku yayin shigar ta fadar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Tawagar Atiku yayin shigar ta fadar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Source: Twitter

Al'ummar tamkar ridi yayin kirdadon zuwan Atiku da Kwankwaso harabar filin wasanni na Sani Abacha

Kano ta yi ja ja wur yayin yakin zaben Atiku

Kano ta yi ja ja wur yayin yakin zaben Atiku
Source: Twitter

Atiku da tawagar sa yayin isar su fadar Sarkin Kano

Atiku da tawagar sa yayin isar su fadar Sarkin Kano
Source: Twitter

Atiku yayin gabatar da jawabai a fadar Sarkin Kano

Atiku yayin gabatar da jawabai a fadar Sarkin Kano
Source: Twitter

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel