Yakin Zabe: An ci kasuwar jar hula a jihar Kano

Yakin Zabe: An ci kasuwar jar hula a jihar Kano

Mun samu cewa, masu sayar da jar Tagiya a yau Lahadi cikin birnin Kano sun dara wajen cin kasuwar su a harabar filin wasanni na Sani Abacha yayin taron yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da aka gudanar.

Rahotanni kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito sun bayyana cewa, jihar Kano ta cika ta batse a yau Lahadi yayin da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe.

Yakin Zabe: An ci kasuwar jar hula a jihar Kano
Yakin Zabe: An ci kasuwar jar hula a jihar Kano
Asali: Twitter

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, sanya jar Tagiya musamman a jihar Kano da wasu jihohin Arewa manuniya ce ta akidar magoya bayan kungiyar Kwankwasiyya da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya assasa.

Wani daga cikin masu sana'ar sayar da jar hula, Mallam Ibrahim Maihula, yayin ganawar sa da manema labarai ya bayyana cewa, a yau cike ya da farin ciki domin kuwa tun gabanin rana ta yi zawali ya sayar da fiye da hulana 250 da ya kasa a harabar filin wasanni na Sani Abacha.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gudanar da yakin zaben sa a jihar Zamfara

Kazalika, wani dan kasuwar na daban, Umar Lawan, da ya taso tun daga karamar hukumar Gwarzo domin halartar taron yakin zaben Atiku, ya ce ya samu nasarar sayar da huluna fiye da 300 da ya kasa a yau cikin birnin Kanon Dabo.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau jhar Kano ta cika ta batse yayin da al'umma suka yi tururuwa tamkar kudan zuma domin halartar taron yakin zaben Atiku wanda masu sharhi suka misalta a matsayi gagarumin taron siyasa da ba a taba samun makamancin sa fadin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng