Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Alkalin Alkalai Ya Yi Bankwana da Duniya

Najeriya Ta Yi Rashi: Tsohon Alkalin Alkalai Ya Yi Bankwana da Duniya

  • Gwamnatin jihar Neja ta sanar da rasuwar tsohon Alkalin Alkalai, Mai Shari’a Muhammad Aliyu Mayaki, yana da shekaru 73 a duniya
  • Gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga bangaren shari’a da jihar Neja baki ɗaya
  • Mayaki ya riƙe matsayin Alkalin Alkalai na jihar Neja daga Agustan 2019 zuwa ritayarsa a Oktoban 2020

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Tsohon Alkalin Alkalai na jihar Neja, Mai Shari’a Muhammad Aliyu Mayaki, ya rasu yana da shekaru 73 a duniya.

Gwamnatin jihar Neja ce ta sanar da rasuwarsa a safiyar ranar Litinin, inda Gwamna Mohammed Umaru Bago ya miƙa saƙon ta'aziyya ga bangaren shari'a da iyalan marigayin.

Tsohon alkalin alkalan Neja ya rasu
Marigayi Muhammad Aliyu Mayaki Hoto: Bologi Ibrahim
Source: Facebook

Babban sakataren yada labaran gwamnan, Bologi Ibrahim, ya sanya sanarwar a shafinsa na Facebook ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga rikicin Ibrahim Masari, Gwamna Radda da 'yan APC, ya bayar da umarni

Gwamna Bago ya yi alhinin rasuwar Mayaki

A cikin saƙon ta'aziyyarsa, Gwamna Bago ya bayyana rasuwar tsohon alkalin a matsayin babban rashi ga tsarin shari'a da jihar Neja.

Gwamnan ya ce marigayin ƙwararren lauya ne mai kishin aiki, jajircewa da ladabi, wanda ya bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa harkokin shari'a.

Ya bayyana cewa Mayaki ya yi amfani da ƙwarewarsa a fannin shari'a wajen inganta tsarin gudanar da shari'o'i da sauye-sauyen da suka dace.

Bago ya ce gudummawar marigayin ba ta tsaya ga jihar Neja kaɗai ba, domin ya taimaka wajen inganta tsarin shari'a a faɗin Najeriya.

Gwamnan ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga Alkalin Alkalai na jihar Neja mai ci, Mai Shari’a Halima Ibrahim Abdulmalik, da iyalan marigayin na kusa da na nesa.

Gudummawar da ya bayar a fannin shari'a

An fi tunawa da marigayin saboda jagorantar kwamitin bincike da tsohon gwamnan Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya kafa domin bincikar yadda tsohon gwamna Abdulkadir Kure, wanda ya rasu, ya gudanar da mulkinsa.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya hango mamakin da za a sha a Arewa saboda Tinubu a zaben 2027

Mayaki ya kuma taɓa zama mamba a kwamitocin shari'a da suka gudanar da wasu ayyukan da suka shafi zaɓe.

Haka kuma, ya jagoranci shari'o'in ƙarar zaɓen gwamnan jihar Cross River a birnin Calabar a shekarar 2015.

Lokacin da ya zama Alkalin Alkalai

An rantsar da Mai Shari’a Muhammad Aliyu Mayaki a matsayin cikakken Alkalin Alkalai na jihar Neja a watan Agustan 2019.

Ya ci gaba da riƙe wannan muƙami har zuwa watan Oktoban 2020, lokacin da ya yi ritaya daga aikin shari'a.

Rasuwarsa ta jawo saƙon ta'aziyya daga Gwamna Bago, wanda ya bayyana irin gudummawar da marigayin ya bayar wajen bunƙasa tsarin shari'a a jihar Neja da Najeriya baki ɗaya.

Gwamna Bago ya yi ta'aziyya
Gwamna Umaru Bago na jihar Neja zaune a ofis Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

Shugaban karamar hukuma ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman, ya yi jimamin rasuwar shugaban ƙaramar hukumar Zaki, Hon. Mas'ud Aliyu Umar.

Marigayin ya rasu ne a yammaci a wani hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Konkiyel, bayan halartar taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APM a babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng