Jakadun Amurka da sauran manyan Kasar waje ba su goyon bayan Buhari - Keyamo

Jakadun Amurka da sauran manyan Kasar waje ba su goyon bayan Buhari - Keyamo

- Kwamitin yakin neman zaben Buhari na APC ta maidawa Amurka martani

- Kasar Amurka tace za a hukunta duk masu kokarin tada kafar baya a zabe

- Festus Keyamo yace Kasashen waje na nuna goyon baya ga Jam’iyyar PDP

Jakadun Amurka da sauran manyan Kasar waje ba su goyon bayan Buhari - Keyamo

APC ta na ganin manyan kasashen Duniya ba su tare da Buhari
Source: Depositphotos

Mun ji cewa kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari watau Festus Keyamo ya zargi jakadan kasar Amurka da kuma wasu manyan kasashen Duniya da nuna son kai a zaben da za ayi a Najeriya a makon nan.

Barista Festus Keyamo (SAN) ya bayyana cewa Stuart Symington wanda shi ne Jakadan Amurka a Najeriya yana nuna goyon baya ne a boye ga ‘dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar a zaben na 2019.

KU KARANTA: Abin da PDP ta gani a Daura wajen yakin neman zaben Atiku

Keyamo yake cewa haka zalika manyan kasashen Turai sun karkata ga Atiku Abubakar na PDP. Mai magana da yawun bakin kwamitin tazarcen shugaban kasar na Najeriya ya maida martani game da wani jawabi na Symington.

Kwanaki Ambasada Stuart Symington ya zari takobin yakar masu kokarin tada rikici a zaben Najeriya da za ayi ‘yan kwanaki masu zuwa. Keyamo yace jawabin kasar Amurkar ya nuna cewa babu adalci a lamarin ta a kan zaben bana.

Babban Lauta Keyamo yayi dogon jawabi inda ya caccaki jakadan na Amurka yana mai maida masa martani inda ya kara da cewa PDP ce ta saba murde zabe a Najeriya. Tuni dai Amurka tace ba ta da ‘dan takara a zaben na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel