2019: Kwankwaso ya hadu da Atiku Abubakar a Garin Abuja
- Sanata Kwankwaso ya kai wa Atiku ziyara jiya a gidan sa da ke Abuja
- Rabiu Sulaiman Bichi su na cikin wadanda su ka yi masa ‘yan rakiya
- Jagoran PDP ya na tare da Atiku wanda ya rasa takarar Shugaban kasa
Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya kai wa ‘dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da Mataimakin sa watau Peter Obi ziyara har gida. Atiku dai ya sha kasa ne a zaben shugaban kasa da aka yi.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya ziyarci Atiku Abubakar ne a gidan sa da ke cikin babban birnin tarayya Abuja. An ga Sanata Kwankwaso a gidan Atiku ne tare da Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano, Injiniya Rabiu Bichi.
KU KARANTA: Mun yanka Bukola Saraki mun birne a siyasa – inji Oshiomhole
Kamar yadda wani Hadimin Sanatan na Kano ta tsakiya ya bayyana mana, tsohon shugaban hukumar Yankin Tarauni da ke cikin Garin Kano watau Honarabul Mukhtar Umar Yerima yana cikin tawagar da ta gana da Atiku a jiya.
Saifullahi Hassan ya bayyana cewa an yi wannan zama ne jiya, sai dai bai bayyanawa jama’a ainihin abin da Alhaji Atiku ya tattauna da tsohon gwamnan na Kano ba. Hakan na zuwa ne dai bayan PDP ta sha kasa a zaben 2019.
Atiku Abubakar ya samu kuri;u kusan 400, 000 ne a jihar Kano inda shi kuma shugaba Buhari wanda ya lashe zaben ya tashi da kuri’u sama da miliyan 1.4. Rabiu Bichi, shi ne shugaban PDP a Kano a yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng