Ana gab da sake yin wata June 12 - Mai kamfen din Atiku

Ana gab da sake yin wata June 12 - Mai kamfen din Atiku

-Wani mai goyan bayan dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ana gab da sake yin June 12 idan de har INEC ta cigaba da ikirarin cewa bata da ma'aji na yanar gizo.

-Sani ya bayyana hakan ne a karshen makon da ya gabata, a lokacin da yake zantawa da yan jarida a Yola, dake jihar Adamawa

-Ya kara da cewa INEC zata bata sunanta idan dai ta cigaba da wannan ikirarin bayan da shedu sun tabbatar da cewa tayi amfani da wannan ma'ajin a zaben 2019

Daya daga cikin masu yima Atiku Abubakar kamfen, Sani Adamu, ya tuhumi hukumar zabe mai zaman kanata (INEC) da cewa ta na kokarin sake aikata abun da ya faru da Abiola, na soke zaben June 12, saboda hukumar na ikirarin ba ta ajiye wani sakamakon zabe a ma’adanar yanar gizo ba a zaben 2019.

Sani ya ce a lokacin da INEC ta gabatar da taron yadda zata gudanar da ayyukanta tun daga 2017-2019, hukumar ta ce ta samar da ma’aji na yanar gizo ga jihohi 36 na fadin kasar nan, da kuma babban birnin tarayya Abuja, kuma babu shakka anyi amfani da wannan ma’ajin na yanar gizo a zaben 2019.

KARANTA WANNAN: Garin Sondi ya zama tsit ba kowa bayan hare-haren da yan bindiga suka kai Taraba

Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da yan jarida a karshen makon da ya gabata a Yola dake a jihar Adamawa.

Sani ya kara da cewa INEC na bata sunanta da mutuncinta ne idan ta cigaba da ikirarin cewa ba ta da wani ma’ajin kuri’u na yanar gizo, inda ya bayyana cewa Atiku da lauyoyin PDP na da hujjoji kwarara da suka tabbatar da cewa maganar da INEC ke yi na cewa bata da ma’aji na yanar gizo ba gaskiya bane.

Sani ya ce “Zan fadi ba tare da wani tsoro ko kokonto ba, tabbas INEC ta sayi kuma ta kafa ma’aji na yanar gizo a dukkan jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya.”

“Shuwagabannin INEC sun samu amincewa akan su mika sakamakon zabe zuwa babbar santa ta tattara zabe ta hanyar amfani da yanar gizo.”

Da yake kara karfafa zancensa, Sani ya ce “PDP da Atiku na da wayau sosai, ina kara fadi, suna da wayau kuma suna da kishi sosai shi yasa suka shirya kwarai da gaske suka samo bayanai game da INEC da duk al’amurranta.”

Sani ya kara da cewa "A daya daga cikin bayanan da Yakubu yayi lokacin da ake shirin zaben 2019, ya bayyanawa duniya cewa ‘wannan ne karo na farko da zamu fara mafani da tsarin tattara sakamakon zabe a hanyar amfani da yanar gizo a zaben 2019.’ "

“Babbar illa ce ga shugabancin INEC su musanta zancen cewa suna amfani da ma’aji na yanar gizo da sauran kaya fasaha.’

“Babbar annoba ce ke shirinn ta afku.” A cewarshi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel