Wasu Kwamishinonin Gwamnan Adamawa yaran Atiku ne – Babachir
Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya a farkon mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, watau Babachir David Lawal ya bayyana dalilan da su ka sa Gwamna Jibrila Bindow ya fadi zaben 2019.
Injiniya Babachir David Lawal yayi hira da Jaridar This Day inda ya tattauna a kan siyasar jihar sa ta Adamawa. Babachir Lawal yace daga cikin abin da ya sa APC ta rasa gwamnan ta shi ne matsalar da aka samu a cikin-gida.
Babachir Lawal yake cewa akwai wadanda ba su tare da Gwamna Jibrila a cikin gwamnatin sa. Lawal yake cewa duk da APC ke mulki a jihar Adamawa, ya zamana cewa wasu Kwamishinonin jihar su na tare ne da Atiku Abubakar.
KU KARANTA:
Tsohon SGF din yake cewa akalla Kwamishinonin jihar Adamawa har su 7 sun nuna cewa su na tare ne da Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP. Haka kuma Lawal yake cewa ‘Diyar gwamnan, tana cikin manyan ‘Yan gidan Atiku.
Mista Babachir Lawal yace sau da-dama gwamna Bindow ya saba nuna cewa gwamnatin sa, gwamnati ce ta Atiku Abubakar. Har ta kai wani babban Hadimin sa ya taba nuna mubaya’ar gwamnatin ta APC ga Atiku da ke PDP mai adawa.
A karshe dai Jibrilla Bindow ya sha kasa ne a hannun Umaru Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP. Jam’iyyar PDP ta samu nasara ne bayan an kai ga zaben cike-gibi. Ahmadu Fintiri ya taba rike kakakin majalisar dokoki na Adamawa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng